Rashin yarda da kai ya sa wasu ƙasashen Yamma ke neman ta da matsaloli

Daga BELLO WANG

Ofishin babban kwamishina mai kula da aikin kare haƙƙin dan Adam na MƊD ya gabatar da wani rahoto dangane da jihar Xijiang ta ƙasar Sin a kwanan baya, wanda ya nuna al’adar ƙasar Amurka da wasu ƙawayenta ta neman yin amfani da batun haƙƙin dan Adam a matsayin wani makami.

Me ya sa a ce haka?
Saboda da farko dai, yadda aka tsara rahoton ya saba ka’idoji. A matsayinsa na daya daga cikin hukumomin MƊD, ya kamata ofishin babban kwamishina mai kula da haƙƙin ɗan Adam ya gudanar da duk wani aiki ne bisa iznin da majalisar kare haƙƙin ɗan Adam ta ba shi, kuma ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata ƙasa ba.

Amma ofishin ya gabatar da wannan rahoto kai tsaye, ba tare da neman samun izini ba, kuma bai taba neman sauraron ra’ayin Sin ba.

Kana ta wannan hanya ya tsoma baki cikin harkokin gida na ƙasar Sin.

Na biyu, shi ne bayanan dake cikin rahoton sun saba da sanarwar da Madam Veronica Bachelet, babbar kwamishinar mai kula da aikin kare haƙƙin ɗan Adam ta MƊD, ta gabatar, a ranar 28 ga watan Mayun bana, bayan da ta kammala ziyararta a jihar Xinjiang ta ƙasar Sin.

Inda ta yaba da ƙasar Sin, kan ƙoƙarinta a fannonin rage talauci, da kare mutane marasa ƙarfi, da yunkurin tabbatar da ingancin haƙƙin ɗan Adam, da dai sauransu.

Haƙiƙa idan mun yi nazari kan mutanen da suke aiki a ofishin babban kwamishina mai kula da aikin haƙƙin ɗan Adam, za a fahimci cewa, zai yi wahala wannan ofishi ya gabatar da wani rahoto na gaskiya.

Saboda ƙasar Amurka da wasu ƙawayenta sun tura ‘yan korensu don su zama manyan jami’an ofishin, inda su kan yin amfani da wasu bayanai marasa gaskiya wajen tsara rahotannin da suke haifar da matsin lamba ga ƙasar Sin, da sauran ƙasashe masu tasowa.

Amma me ya sa ƙasar Amurka da abokanta ke ƙoƙarin yin amfani da damammaki daban daban wajen shafa kashin kaza ga ƙasar Sin, da kafa shingaye ga sauran ƙasashen masu tasowa? A ganina, suna haka ne domin ba su yarda da kansu ba.

Ƙasashen yammacin duniya na ganin cewa, dole ne ƙasashe masu tasowa su bi tsarin dimokuraɗiyya irin nasu, da zama ƙarƙashin jagorancinsu, kafin su iya samun ci gaba mai ɗorewa.

Sai dai ƙasar Sin, a ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin, ta zabi hanyar da ta tsara da kanta kuma da dace da yanayin al’ummarta, inda ta ɗauki tsarin gurguzu mai siffar musamman ta Sin, tare da samun babban ci gaba, cikin gomman shekarun da suka wuce.

Wannan ya sa ƙasashen yamma kaɗuwa, saboda yadda ƙasar Sin ta samu nasara ta nuna cewa, ƙasashe masu tasowa za su iya raya kansu, ta hanyar musamman da suka zaɓa, maimakon ci gaba da bin umarnin ƙasashen yamma.

Wannan damuwa ta sa ƙasar Amurka da wasu ƙawayenta ke ƙoƙarin gogayya da ƙasar Sin, da haifar da matsaloli a harkoki masu alaka da haƙƙin ɗan Adam, da jihar Xinjiang, da yankin Taiwan na ƙasar Sin, da dai sauransu, don hana ƙasar Sin samun ci gaba.

Sai dai ƙasar Sin ta yi ta samun nasarar daidaita waɗannan matsaloli, bisa cikakken imanin da take da shi a kan turbar da ta zaɓa.

Haka kuma Sinawa suna iya haƙuri da mabambantan ra’ayoyin da ake samu a duniya, da iya tinkarar duk wani ƙalubalen da suka kunno kai yayin da suke ƙoƙarin raya ƙasarsu.

A nasu ɓangare, ƙasashe masu tasowa su ma sun fara ganin yanayin rashin adalci na tsare-tsaren kula da harkokin duniya da ƙasashen yamma suka gabatar, wannan ya sa suke ƙoƙarin nemo hanyar raya kansu wadda ta dace da yanayin da suke ciki.

Wannan wani muhimmin yanayi ne da muke fuskanta a wannan zamanin da muke ciki.