Yankin Zanzibar na Tanzaniya ya karrama tawagar likitocin Ƙasar Sin da lambar yabo saboda hidmar da suka bayar

Daga CMG HAUSA

Shugaban yankin Zanzibar na ƙasar Tanzania, Hussein Ali Mwinyi a ranar Asabar din da ta gabata ya karrama mambobi 21 na tawagar likitocin ƙasar Sin da lambar yabo, saboda hidimar aikin jinya da suka bayar na tsawon shekara ɗaya a tsibirin na Zanzibar.

Mwinyi ya shaida wa tawagar likitocin na ƙasar Sin yayin da yake ban kwana da su a gidan gwamnatin Zanzibar cewa, ana da dalilai masu tarin yawa na miƙa godiya ga irin gagarumin aikin da likitocin ƙasar Sin suka yi na tabbatar da cewa, jama’ar Zanzibar sun samu hidimar ayyukan kiwon lafiya mafi kyau a cikin shekara guda da ta gabata.

Ya bayyana cewa, tawagar likitocin ƙasar Sin, sun samar da hidima fiye da jinyar mutane.

Haka kuma tawagar ta samar da kayan aikin jinya da magunguna, baya ga horar da ma’aikatan lafiya dake yankin.

Shugaba Mwinyi ya godewa ƙasar Sin, kan yadda ta tura tawagogin likitoci zuwa yankin, yana mai cewa, tawagogin likitocin ƙasar Sin, sun taimaka wajen ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar ƙasar tare da ceto rayukan ɗaruruwan mutane.

Tun bayan zuwan tawagar likitocin ƙasar Sin ta 31 Zanzibar a cikin watan Satumban da ya gabata, tawagar ta samar da hidimar jinya ga majinyata fiye da 6,000 a tsawon shekara guda da ta shafe tana wannan aiki.

Mai fassara: Ibrahim