Nancy Ajram: Sarauniyar Mawaƙan Larabawa

Daga AISHA ASAS

Kiɗa da waƙa wata daɗaɗɗiyar al’ada ce ko in ce ɗab’i da ba kasafai kake samun al’ummar da ba ta da irin nata da ta ke nishaɗanta da ita ba. Wannan ne ya sa duk inda ka ratsa za ka tarar da kiɗa da waƙa ya rigaka zuwa, sai dai ka tarar da ba irin wanda ka baro ne a inda ka fito ba.

Za mu iya kiran waƙa a matsayin wasiƙu zuwa ga zukatan mutane, hakan zai sa da wahala ka rasa wadda aka yi domin taka zuciyar. Kazalika bincike ya tabbatar waƙa na kan gaba a hanyoyin kawar da damuwa, saboda soyayyar da ke tsakanin ta da zukatan mutane.

Idan muka yi duba da waƙoƙin da suka shuɗe, a lokacin da ake yin waƙar a baki ba tare da taimakon lasifika ba, yayin da mutane ke amfani da hannayensu don yi masu kiɗa. Aka wuce wannan zamani, zuwa zamanin da lasifika ta samu, kayan kiɗa suka zo, har aka kai da za ka iya yin waƙa a wani wurin da aka killace, aka zuba kayan kiɗan, sannan a fitar da ita ga jama’a, wato sitidiyo.

Nancy tare da ‘yan uwanta

Daga nan kuma sai ci gaba ake samu, ta hanyar kayan kiɗan da ita kanta waƙar da kuma muryoyin masu waƙar.

Baya ga waƙoƙi na gida da kowacce al’umma ta ke da irin nata, akan samu kamanceceniya a waƙoƙin da suke da banbancin yare, matuƙar sun yi riƙo da zamani ko in ce salo irin na Turawa, waɗanda suka zama abin koyi a wannan lokaci.

Da irin wannan salo ne da yawa daga cikin mawaƙa suka yi suna a duniya, duk da cewa da yawa daga cikinsu ba sa amfani da yaren Turanci.

A wannan sati, shafin Nishaɗi zai kawo ma ku tarihin ɗaya daga cikin mawaƙa da suka karaɗe duniya da amon sautinsu, wadda ta samu wurin zama a duniyar waƙoƙi, har ta kai matsayin da ake kiranta da Sarauniyar Mawaƙan Larabawa, wato Nancy Nabil Ajram. A sha karatu lafiya:

Nancy Ajram yar asalin Ƙasar Labanon ce, mawaƙiyar da ta kafa tarihi a waƙoƙin Larabci, kasancewar ta fara waƙa tun tana da shekaru 13, kuma tun a lokacin waƙoƙin nata ke samun karvuya.

Nan y tare da mahaifiyarta

Duk da cewa, waƙa bata zama baƙuwa ga Nancy kafin ta kai shekara 13 ba, domin an tabbatar da ta fara waƙa ne tun tana shekara takwas da haihuwa, ta fara ne tare da kakarta, yayin da ta ci gaba ta gasar waƙa ta yara da ke gudana a gidajen talabijin biyu a lokacin, TL da kuma LBC. Sai dai a lokacin da ta kai 13 ne ta fara hawa kujerar waɗanda ake kira da mawaƙa a idon duniya.

Duk wannan al’amarin ya faru ne da taimakon mahaifinta, Nabil Ajram da ya zame mata ɗan jagora kan lamarin tare da tsaya mata a duk inda akae buƙata.

An haifi Nancy a ranar 16 ga watan Mayu, 1983, a Achrafieh, Beiruf na Ƙasar Labanon. Mawaƙiya ce da ta fitar da mawaƙan Larabawa, kasancewar ta wadda ta fi kowacce mawaƙiyar da ke waƙa da yaren Larabci suna da shahara a duniya.

Duk da cewa ta fito a wani ɓangare na Larabawa, hakan bai hana ta ratsa sauran ƙasashen da ke jin Larabci tare kuma da samarwa waƙoƙinta muhallin zama a cikin zukatansu. Ba ta tsaya iya nan ba, Nancy ta kasance jerin mawaƙan Larabawa da suka tallata waƙoƙin Larabci ga duniya, kuma duniyar ta karɓe su da hannu biyu. Dalilin kenan da ya sa ake mata kirari da ‘Sarauniyar Mawaƙan Larabawa’.

Baya ga waƙa, Nancy ta kasance ‘yar kasuwa kuma mai gabatar da wasu shirye-shirye na musamman a gidajen tallabijin kamar ‘Arab Idol’ da makamantan su.

Wasu na ganin cewar, Nancy ce ta farfaɗo tare da dawo da ƙimar waƙoƙin Larabci a idon duniya, bayan da suka yi dogon suma.

Nancy tare da mahaifinta

A lokacin da ta ke shekaru 15, Nancy ta samu kwantiragi da shahararren kamfanin nan na EMI. Kuma ta fitar da kundin waƙoƙinta a shekarar, wato shekara ta 1998. Yayin da kundinta na biyu mai suna ‘Sheel Oyoonak Anni’ ya zo a shekara ta 2001.

Duk da kasancewar ta a shekaraun yarinta bai hanata samun kujerar zama a ‘da’irar’ shahararrun mawaƙa da suka amsa sunansu ba tare kuma da bata girma albarkacin baiwar da ta ke da ita. kazalika ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke taimaka wa al’umma ko wayar da kansu, waɗanda ke amfani da shararrun mutane don tallata manufofinsu ko bayar da taimakonsu, ba su duba ƙarancin shekarunta ba wurin saka ta cikin waɗanda suke aiki da su kan manufofinsu. Don haka ta zama yarinya ta farko da ta samu kanta a wannan matsayi.

Idan muka koma ɓangaren karramawa ko lambar yabo, ba sai na sanar da mai karatu ba, zai iya kwatanta wa ko ta hanyar duba da matsayinta a nan gida Nijeriya. Idan za ka samu ma’abuci son waƙoƙin Larabawa, da ƙyar ka ji bai ambato Nancy a jerin farko na mawaƙan da ya fi so ba. Asalima ko waɗanda ba su damu da waƙoƙin Larabawa ba suna sauraron waƙoƙinta ba tare da sanin wadda ta yi suba, kamar waƙar ‘Ya Tab-tab’, ‘Yeeh’ da kuma ‘Lau kan ta hub’.

Da yawa mutane na amfani da waƙoƙin nan a cikin jerin waƙoƙin da suke sauraro.

Tun tana da ƙurciya ta fara samun lambar yabo tare da karramawa, kuma ta ke cinye gasar waƙoƙi a ƙasashen Larabawa. Kazalika ta yi nasarar zama Gwarzuwar Mawaƙa ta duniya a ɓangaren Gabas ta Tsakiya, wanda yanzu haka ta ke a wannan matsayi. Kuma ita ce mawaƙiya mai ƙarancin shekaru da ta taɓa samun wannan lambar yabo.

Idan mun koma ɓangaren iyali, Nancy Nabil Ajram, na daga cikin mawaƙan da suka yi nasarar samun albarkar aure, wato ‘ya’ya. Uwa ce ga ‘ya’ya uku, Milal, Lya, da kuma Ella, waɗanda ta haifa da mijinta Fadi El Hachem, wanda ya kasance likitan haƙora. Sun yi aure a shekara ta 2008.

Nancy tare da iyalinta

Ita ce ‘ya ta farko a wurin mahaifanta, sannan tana da ƙanne biyu, Nadine Ajram da kuma Nabil Ajram.