Daga BASHIR ISAH
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NAFDAC), ta yi gargadin a daina sayarwa da kuma amfani da wasu magungunan tari na yara da aka gano suna da illa.
Ta ce shagunan magungunan da ke da irin wannan magani su hanzarta tattara su sannan su mika wa ofishin NAFDAC mafi kusa.
Shugabar Hukumar, Farfesa Moji Adeyeye ce ta yi wannan gargadi a wajen wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
Gargadin nata na zuwa ne biyo bayan gano wasu gurbatattun magungunan tari guda hudu da aka yi a kasar Gambiya wanda suka yi sanadiyar mutuwar yara 66 a kasar.
Ta ce gurbatattun magungunan sun hada da; Promethazine oral solution da Kofexmalin baby cough syrup da Makoff baby cough syrup da kuma Magrip N cold syrup.
Ta kara da cewa, bincike ya gano kamfanin hada magungunan da ke kasar Indiya, Maiden Pharmaceuticals Limited, shi ne masarrafin magungunan.
