Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wasu ’yan bindiga sun kashe ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa Abuja zuwa Kaduna da aka sako kwanan nan akan hanyar Funtua zuwa Gusau da ke kan hanyarsa ta komawa mahaifarsa a Jihar Kebbi a ranar Asabar.
Wanda aka kashe ɗin wanda ba a bayyana sunansa ba ya shafe sama da watanni shida a hannun ’yan ta’adda bayan harin da aka kai kan hanyar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022.
An kashe sa ne a hanyarsa ta zuwa mahaifarsa a Jihar Kebbi tare da ’yan uwansa waɗanda hukumomi a Jihar Kaduna suka dawo da shi bayan ceto su a makon jiya.
An kashe shi ne kwanaki uku bayan da ƙungiyar Ansarul reshen ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta sako shi bayan ya kwashe sama da kwanaki 190 a hannunsu.
An tattaro cewa, ’yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da ɗaya daga cikin ’yan uwansa da ke tuƙa motar zuwa wani wuri da ba a san inda suke ba har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoton.
Kashi na larshe na waɗanda aka yi garkuwa da su wanda mamacin na cikin su sun sake samun ’yancinsu a makon da ya gabata a ranar Laraba, 5 ga Oktoba, 2022 bayan watanni shida a hannunsu.
An kuma tattaro cewa, ’yan bindiga sun harbi marigayin kansa a kan titin Funtuwa zuwa Gusau mai cike da cunkoson jama’a kuma ya mutu sa’o’i kaɗan bayan an garzaya da shi babban asibitin Tsafe, a kan babbar hanyar.
Tuni dai aka binne shi a garinsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
