Ranar Malamai: Tica uban karatu, cuta ko cutarwa?

Daga AMINA HASSAN ABDUSSALAM

Idan na kalli halin da malaman jami’a suke, sai na ga kamar haka malaman Sakandire da firamare suke, sai dai su ba su da murya mai amo irin ta ASUU.

  1. Zan fara da yanayin koyo da koyarwa a makarantun ƙasa da na tsakiya. Yaushe rabon da a tura malamai bita don inganta koyo da koyarwa idan ka cire ire-iren bitar da ƙasashen waje ke yi ta hanyar tallafa wa ilimi a Najeriya?
  2. Kashi 80% na makarantun babu kayan aiki, kayan aiki ba wai yana nufin kayan record ɗin malami kaɗai ba, ɗaliban ba su da litattafai (textbooks) ‘ya’yan talakawa ne ba za su iya siya ba. Da yawan makarantu suna siyan alli daga kuɗin harajin masu talla.

A yau idan ka ba wa ɗan aji biyar ko shida takarda da biro ka zaunar da shi a kan kujera da tebur ka ce ya yi rubutu, ba zai iya ba, zai ɗora ne akan cinyarsa saboda bai saba da zama a kujera da tebur ba don babu.

In ka ga makaranta an gyara ta fes, an wadata wasu ajujuwa da abin zama to daga tsaffin ɗalibai ne.

  1. Rashin kyakkyawan albashi yana daga cikin abin da ke ci wa malamai tuwo a ƙwarya, malamin da ke matakin albashi 13 a firamare albashin sa bai wuce ₦70,000 zuwa ₦100,000 ya danganta da jihar da kake. Sannan za ka tarar ya kai shekara 20 yana aiki, shima ya danganta da matakin takardar da ya fara aiki da ita.
  2. Daga cikin kasafin kuɗin ƙasa kaso nawa ake ware wa ilimi a Najeriya? A 2022 ɗin nan kaso 5.5% aka ware wa ɓangaren ilimi maimakon 8.4% da UNESCO ta shawarta, a da can ma an tava cewa kamata ya yi Najeriya ta dinga ware wa ilimi kaso 26% na jimlar kasafin kuɗin ƙasa. Amma jiya i yau.
  3. Abu na gaba da ya ƙara taɓarɓarewar ilimi a ƙasar nan shi ne, haɗa ɓangaren da siyasa, tun daga matakin ƙasa har zuwa sama. Ba a duba cancanta, ƙwarewa, iyawa, dacewa da ma sauran siffofi na halaye da na kwanya da ɗabi’a, hanya tana sanya wa a ɗauki kowa ma ya koyar.

Siyasa ta sa an ɗau ‘yan ƙwaya su koyar a Sakandire da firamare, siyasa ta sa an ɗau malamai da takardun bogi, a can sama kuma siyasar da hanya ɗin dai sun sa an ɗau waɗanda ba su da dabarun koyarwa aiki.

  1. Jami’a tana da ASUU da a yau mun ga yadda take amsar gashi a hannun gwamnati, amma da ka mutu rago gara ka mutu jarumi, ita kuwa NUT ina muryar ta? Ta ma isa ta yi magana a kan haƙƙoƙin ‘ya’yanta? Ina, ba ta isa ba! Kullum sai dai su yi ta rarrashin kansu da cewa ladansu na lahira, ba cin daɗi a duniya, ƙaddararsu kenan.
  2. Duk waɗannan rashin cigaban ne ya sa daga cikin ƙwararrun malamai suka yi la’asar, har suke yi wai aikin wani irin riƙo, ba a ma maganar waɗanda ba su iya aikin ba.

Muna dai gani yadda matasa ke ƙetarewa zuwa neman ilimi a wasu ƙasashen, wasu daga nan kuma shike nan su da Najeriya sai dai ziyara. Wasu na kusa da ni da na zanta da su cewa me ya sa ba za su yi karatun a jami’o’i masu zaman kansu na ƙasar nan ba? Sai suka ce da ni “Tsaron fa? Ai babu garanti!”

Da gwamnatin Najeriya ta tserar da mutuncin ilimi da tsaron ƙasar nan da ba haka ba, da yanzu wani labarin ake yi.

Amina Hasan Abdussalam (AHA), marubuciya ce, kuma ‘yar ƙasa mai bayyana ra’ayi.