Budurwa ta kashe saurayinta a Nasarawa

Spread the love

An damƙe wata mata mai shekara 30 kan zargin yin amfani da wuƙa ta kashe saurayinta a yankin Maraba da ke Jihar Nasarawa.

Kakakin ’Yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce, matar ta kashe saurayin nata ne bayan faɗa ya kaure a tsakaninsu.

Ya ce, yanzu, “tana hannu kuma an kwace wuƙar da ta yi amfani da ita wajen aikata kisan, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, Adesina Soyemi.

A cewarsa, sun damƙe matar ne bayan ta yi ɗanyen aiki a Ungwan Gwari, Karamar Hukumar Karu ta jihar.

“An miƙa ta ga Babban Sashen Binciken Manyan Laifuka da ke Lafia domin zurfafa bincike sannan a gurfanar da ita a gaban kotu domin zama izina ga wasu,” inji shi.

By Editor