Sabuwar Ƙasar Sin ta ba ‘yan uwanta na nahiyar Afirka alfahari

Spread the love

Daga BELLO WANG

Wasu shekaru 51 da suka wuce, wato a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, aka zartas da wani ƙuduri a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), inda aka maido da kujerar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin (sabuwar ƙasar Sin) a majalisar.

Wani bidiyon da aka ɗauka a lokacin ya nuna yadda wasu jami’an ƙasashen Afirka da suka halarci taron MƊD suka yi matukar murnar ganin yadda sabuwar ƙasar Sin ta samu wannan nasara.

Tsohon shugaban ƙasar Sin Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ‘yan uwa na nahiyar Afirka sun ɗauki sabuwar ƙasar Sin, sun kai ta cikin MƊD.

Haƙiƙa cikin ƙasashe 23 da suka gabatar da buƙatar shigar da sabuwar ƙasar Sin cikin MƊD, fiye da rabinsu ƙasashe ne daga nahiyar Afirka.

Sa’an nan, a lokacin da aka jefa ƙuri’a kan batun a majalisar, an jefa kuri’un amincewa 76, inda kuri’u 26, ko kuma mu ce kashi 1 bisa kashi 3 daga cikinsu, kuri’u ne da ƙasashen Afirka suka jefa.

Amma mene ne dalilin da ya sa ƙasashen Afirka suka nuna goyon baya ga sabuwar ƙasar Sin don ganin komawarta cikin MƊD?

Shi ne domin a lokacin, ko da yake sabuwar ba a maido da kujerar ƙasar Sin cikin MƊD ba tukuna, sakamakon yunkurin ƙasar Amurka na hana ruwa gudu game da batun, duk da haka, sabuwar ƙasar Sin ta yi ƙoƙarin kare adalci a duniya, inda ƙasar ta gabatar da ƙa’idoji biyar na zama tare cikin sulhu, da gina layin dogon da ya haɗa Tanzania da Zambia kyauta, da ba da taimako ga ɗimbin ƙasashen dake nahiyoyin Afirka, da Asia, da Latin Amurka, a fannin yaƙar ‘yan mulkin mallaka, da neman ‘yancin kansu.

Zuwa yanzu, wasu shekaru 51 sun shuɗe. Idan aka waiwayi baya, ko zabin da ƙasashen Afirka suka yi ya yi daidai?

Za a tuna da cewa, cikin shekaru 51 da suka wuce, ƙasar Sin ta halarci kusan dukkan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na tsakanin gwamnatoci, da sa hannu kan yarjeniyoyin ƙasa da ƙasa fiye da 600.

Kana ƙasar ta zama ta biyu a fannin yawan samar da kuɗi ga MƊD. Haka zalika, ta tura sojoji fiye da dubu 50, don gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a wurare daban daban na duniya.

Ba za a manta da yadda ƙasar Sin ta samar da gudunmowa ga aikin daidaita kundin tsarin MƊD don tabbatar wa ƙasashe masu tasowa damar tura wakilansu don zama babban sakataren majalisar ba. Abin da ya ɗaukaka matsayin ƙasashe masu tasowa, da ba su ƙarin ikon faɗa a ji.

Sa’an nan a taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin mai riƙe da ragamar mulki a ƙasar, Xi Jinping, babban magatakardan jam’iyyar, kana shugaban ƙasar Sin, ya nanata babbar manufar ƙasar Sin ta kare zaman lafiya a duniya, da bai wa ƙasashe daban daban damar samun ci gaba tare.

Hakan ma ya shaida muhimmiyar rawar da ƙasar Sin ke takawa a duniya, inda take ƙoƙarin neman ganin kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Vernon Mwanga, wani tsohon jami’in diplomasiya ne na ƙasar zambia, wanda ya taba jefa ƙuri’ar amincewa don taimakawa ƙasar Sin komawa cikin MƊD.

Yanzu, da ya waiwayi aikin da ya yi a lokacin, ya gaya ma ‘yan jaridu cewa, “wannan abun alfahari ne mafi muhimmanci da na taba yi a duk tsawon rayuwata”.

By Editor