Daga CMG HAUSA
Mamban majalisar gudunarwar ƙasar Sin kuma Ministan harkokin wajen ƙasar Sin, Wang Yi ya halarci taron ƙasa da ƙasa kan fasahar tagwaita irin shinkafa da wadatar abinci a duniya, wanda aka yi jiya a birnin Beijing.
A cewar Wang Yi, babban taron wakilan JKS karo na 20 da aka kammala a baya-bayan nan, ya bayyana cewa, ƙasar Sin za ta bayar da sabbin gudunmuwa ga ci gaban bil Adama ta hanyar zamanantar da kanta, inda sabon ci gaban da ƙasar za ta samu, za ta samar da sabbin damarmaki ga duniya.
Ya ƙara da cewa, fasahar tagwaita irin shinkafa, wani ci gaba ne a tarihin kimiyya da fasahar aikin gona na ƙasar Sin, wadda ba taimakawa Sin wajen samun wadatar abinci kaɗai ta yi ba, har ma da bayar da gagarumar gudunmuwa wajen warware matsalar ƙarancin abinci a duniya.
Ya ci gaba da cewa, Sin ta ɗauki wadatar abinci a matsayin ɗaya daga cikin ɓangarorin da take ba muhimmanci a shirin raya duniya, yana mai cewa a shirye Sin take ta haɗa hannu da sauran ƙasashe da hukumomin ƙasa da ƙasa, domin bayar da ƙarin gudunmuwa ga tabbatar da wadatar abinci a duniya da cimma muradun ci gaba masu ɗorewa na shekarar 2030.
Mai Fassara: Fa’iza Mustapha
