Nazarce-nazarce sun nuna yadda aka samu ƙarin kyautatuwar ra’ayin al’ummun ƙasashe masu tasowa game da Sin

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Wasu nazarce-nazarce biyu da jami’ar Cambridge ta Birtaniya ta gudanar, sun nuna cewa, jama’ar ƙasashe masu tasowa na ƙara bayyana kyawawan ra’ayoyi game da ƙasar Sin.

A ƙarshen watan Oktoba, cibiyar nazarin makomar demokraɗiyya dake jami’ar Cambridge, ta tattara wasu nazarce-nazarce 30 da suka shafi ƙasashe da yankuna 137, wadanda ke da kaso 97 na al’ummar duniya, inda suka gano cewa, a ƙasashe masu tasowa da suka haɗa da na Latin Amurka da Afrika da Asiya, an samu kyautatuwar ra’ayi game da ƙasar Sin cikin shekaru 2 da suka gabata.

Inda a tsakanin al’ummar Nijeriya, ƙarin ya kai kaso 83 a bana, daga kaso 68 a shekarar 2021.

Haka zalika, wata ƙuri’ar ra’ayin matasa a ƙasashen Afrika, ta nuna cewa, kaso 76 daga cikinsu, na ganin tasirin Sin a duniya a matsayin mai kyau.

Nazarce-nazarcen sun mayar da hankali ne kan hira ta fuska da fuska da aka yi da matasan da shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 24 a ƙasashen Afrika 15.

Kayayyakin Sin masu inganci da arha da jarin ƙasar kan ababen more rayuwa a nahiyar da samar da guraben ayyukan yi ga al’umma, na daga cikin dalilan da suka sa mutanen suka bayyana kyakkyawan ra’ayin da suke da shi game da ƙasar Sin.

Mai Fassara: Fa’iza Mustapha

By Editor