SSS ta mamaye CBN, ta karbe ikon ofishin Emefiele

Spread the love

Daga WAKILINMU

A ranar Litinin jami’an hukumar tsaro ta SSS suka mamaye ginin hedkwatar Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ke Abuja inda suka karɓe ikon ofishin Gwamnan Bankin, Godwin Emefiele.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar ba yau SSS ta fara farautar Emefiele ba kan zargin almundahana.

A baya, hukumar SSS ta buƙaci kotu ta ba ta izinin tsare Emefiele amma ya zamana ba ya ƙasa sakamakon hutu da ya tafi wanda zai ƙare ranar Talata, 17 ga Janairu.

Sai dai a Disamban da ya gabata Babbar Kotun Abuja ta haramta wa SSS cafke Emefiele, ko tsare shi, ko kuma riƙe shi.

Majiyarmu ta ce jami’an SSS sun isa hedikwatar CBN a ranar Litinin din ne da motoci kimanin 20 ɗauke da jama’ai da makamai.

Haka nan, jami’an sun hana ɗaukacin ma’aikatan CBN shiga ofishin Emefiele.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, kakakin SSS, Peter Afunanya, bai kai ga cewa uffan ba.

By Editor