Da Ɗumi-ɗumi: DSS ta ƙaryata mamaye CBN

Hukumar tsaro ta DSS ta ce, ba ta mamaye hedikwatar CBN da ke Abuja ba kamar yadda rahoto ya karaɗe wasu kafafen yaɗa labarai.

DSS ta bayyana haka ne cikin taƙaitacciyar sanarwar da ta fitar ta bakin kakakinta, Peter Afunanya, ranar Litinin a Abuja.

Afunanya ya ce hankalin DSS ya kai kan wani rahoton ƙarya da aka yaɗa wanda ke nuni da jami’an hukumar sun mamaye hedikwatar CBN da ke Abuja.

Tun farko Daily Nigerian ta rawaito jami’an DSS sun mamaye CBN tare da karɓe ikon ofishin Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, inda aka ce sun hana ma’aikata shiga ofishin.