Mace da kwalliya aka san ta

Daga MARYAM

Mace da kwalliya aka san ta, wacce ba ta kwalliya ba ta cika mace a zahirin ta ba. Babu mace mummuna sai dai macen da ba ta kwalliya.

Sai dai kwalliyar ma kala-kala ce, wasu kwalliyar suna suka tara, don ba zai yiwu a shafa foundation a fuskar da ba ta da haske a yi tsammanin samun kwalliyar raɗau ba. In na ce haske ba ina nufin farin fata ba, ina nufin ƙyalli na gyara.

Yawancin mutanenmu suna tsorata da maganar kayan gyaran jiki don tsadar su, a rashin saninsu da kuɗi ƙalilan za su samu biyan buƙata da kayanmu na gargajiyan da kullum muke ta’ammali da su. Misali: riɗi, lalle, ɓawon kwai, lemon tsami da sauran su.

Inda matsalar yake, ya ake sarrafa waɗannan abubuwa har a samu biyan buƙata? Ku biyo ni don jin sirrin.

  1. Lalle
  2. Ɗanyen rixɗi

A samu ɗanyen riɗi a gyara shi, a daka sosai ya yi gari. A zuba ƙullin lalle a daka wuri guda. Bayan sun haɗe, a juye a ajiye a roba don amfanin yau da kullum.

Yadda za ki yi amfani da shi:-

A ɗibi daidai yadda zai isa fuska, a kwaɓa da ruwa, a shafa. Bayan awa guda, a dirje kafin a wanke. A ranar farko za a ga ci gaba.