Emefiele ya koma bakin aiki bayan kammala hutu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya koma bakin aiki bayan kammala hutun da ya ɗauka.

Sanarwar da CBN ya fitar ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Daraktan sadarwa na bankin, Osita Nwanisobi, ta ce a Disamban da ya shuɗe Emefiele ya ɗauki hutu.

Kuma ya dawo bakin aiki da sabbin dabaru kafin taron farko na Kwamitin Dokar Kuɗi (MPC) wanda zai gudana ran 23 zuwa 24 ga Janairun 2023.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Emefiele na jaddada ƙoƙarinsa wajen aiwatar da ayyukan da suka rataya a kansa daidai da doka da kuma umarnin Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

A ƙarshe, Daraktan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da mara wa CBN baya dangane da tsare-tsarensa na burin ganin an cimma daidaito a fannin hada-hadar kuɗi na ƙasar.