CBN ya tswaita wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira da kwana 10

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita wa’adin daina karbar tsoffin takardun Naira ya zuwa 10 ga Fabrairu, 2023.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya ba da sanarwar ƙarin wa’adin a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce, sai da CBN ya nemi amincewar Shugaba Muhammadu Buhari kafin ɗaukar matakin tswaita wa’adin da kwana 10.

“La’akari da halin da ake ciki, mun nemi yardar Shugaban Ƙasa kan waɗannan abubuwa: Sahalewar tswaita wa’adin da kwana 10 daga 31 ga Janairu zuwa 10 ga Fabrairu don ba ba da damar ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira daga hannun ‘yan Nijeriya.

“Ƙarin kwana bakwai daga ran 10 ga Fabrairu zuwa 17 ga Fabrairu wanda ya yi daidai da Dokar CBN Sasahe na 20(3) da 22 don bai wa ‘yan ƙasa damar kai tsoffin takardun Naira CBN bayan ƙarewar wa’adin da aka ƙayyade,” in ji sanarwar.

Haka nan, Emefiele ya nemi haɗin kan ‘yan ƙasa wajen tabbatar da nasara wajen ɗabbaƙa tsare-tsaren CBN.

Kafin wannan lokaci, ‘yan Nijeriya na kokawa kan baƙar wahalar da suke sha wajen miƙa tsoffin takardun Naira da mallakar sabbin takardun a bankuna.

By Editor