Canjin kuɗi: Sanata Adamu ya goyi bayan gwamnonin APC

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu tare da Ƙungiyar Gwamnoni (PGF), sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi biyayya ga umarnin Kotun Ƙoli kan batun canjin kuɗi.

Kiran na zuwa ne a lokacin da Adamu ya yi zama da gwamnonin na APC ranar Lahadi a Abuja kan ‘yar tsamar da ke tsakanin gwamnonin da Fadar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar.

Da fari Kotun Ƙoli ta bai wa CBN umarnin dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗi, wato N200, N500 da kuma N1,000 amma Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce babu gudu ba ja da baya game da wa’adin.

Sai dai kuma a jawabinsa ga ‘yan ƙasa a ranar Alhamis, Shugaba Buhari ya tsawaita wa’adin amfani da N200 kaɗai da kwana 60 domin rage wa ‘yan ƙasa raɗaɗin ƙarancin kuɗin da suke fuskanta, lamarin da ya haifar da suka daga wasu ‘yan majalisarsa.

Gwamnonin APC da suka haɗa da Nasir El-Rufai (Kaduna), Yahaya Bello (Kogi), Bello Matawalle (Zamfara), Abdullahi Ganduje (Kano) da Dapo Abiodun (Ogun) na daga cikin waɗan da suka shigar da ƙara Kotun Ƙoli kan Gwamnatin Tarayya don rashin gamsuwa da matsayar Shugaba Buhari.

Da yake karanto matsayar taron nasu, Sanata Adamu ya ce, “Mun sani cewa sake fasalin kuɗin ya jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali.

“Muna kira ga Babban Lauyan Ƙasa da Gwamnsm CBN da su martaba umarnin Kotun Ƙoli na a bari a ci gaba da amfanin da tsofaffin kuɗi na wucin-gadi.

“Taron na kira ga Shugaba Buhari da ya sa baki don magance matsalar da haifar wa ‘yan Nijeriya matsin rayuwa.”

Gwamnati dai ta ce ta ɗauki matakin canjin kuɗin ne domin yaƙi da rashawa da kuma siyasar kuɗi a ƙasar.

By Editor