Muƙamin Minista: Tinubu ya maye gurbin El-Rufai da Balarabe

Spread the love

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya zaɓi Abbas Balarabe don maye gurbin tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin minista.

Hakan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Tinubu ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Talata

Haka nan, Dr Jamila Ibrahim da Ayodele Olawande na daga cikin sunayen da wasiƙar ta ƙunsa wanda Tinunu ke neman majalisar ta tabbatar da su a matsayin ministocin matasa.

Idan ba a manta ba, a watan Agustan da ya gabata Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da ministoci 45, amma ta ƙi tabbatar da wasu uku, ciki har da toshon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

By Editor