Hon. Hassan El Ben Jaz ya raba wa mutum 3210 tallafin abinci a Yobe

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

A yunƙurin sa wajen rage wa al’ummar mazaɓarsa wahalhalun da cire tallafin man fetur ya jefa jama’a, ɗan majalisa a Mazaɓar Bade/Jakusko a jihar Yobe, a zauren majalisar wakilai ta ƙasa, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Hon. Hassan Jakduwa KaiKaku (El Ben Jaz) ya ƙaddamar da rabon kayan abinci, tare da takin zamani ga manoma a mazaɓarsa dake jihar Yobe.

A jawabinsa wajen ƙaddamar da rabon kayan a Gashuwa, Hon. Hassan El Ben Jaz, wanda Malam Salisu Jawi ya wakilta a taron, ya ce aƙalla mutum 3210 ne a mazaɓarsa za su ci gajiyar tallafin a ƙananan hukumomin Bade da Jakusko.

Ya ƙara da cewa, ya raba kayan abincin domin rage raɗaɗin da al’ummar mazaɓarsa ke fuskanta sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.

“Kayan abincin sun haɗa da gero, masara, dawa, wake da takin zamani sumfurin MPK, don rage wahalhalun da jama’a suke fuskanta sakamakon matakin da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta aiwatar na cire tallafin man fetur,” In ji Malam Hassan.

A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin raba kayan, Malam Yusuf Ibrahim ya ce, sun ware buhunan kayan abinci tare da takin zamani 1605 ga kowace ƙaramar hukuma; Bade da Jakusko, kamar yadda ɗan majalisar ya tsara.

“Kowace gunduma (ward) an ware mata buhunan abinci da taki 145, sannan kowacce unguwa za ta samu buhun gero 40, buhun masara 40, dawa 40, buhun wake 20, da taki buhu 5, wanda ya kama buhu 145 a kowace gunduma.”

“A matsayinmu na yan jam’iyyar PDP, salon rabon kayan tallafin mu na daban ne, saboda mu na koyi da jagoranmu, Hon. Malam Hassan Jakduwa, wanda hakan sanannen abu ne daga cikin kyawawan halayensa na karimci da kyautata wa kowa ba tare da nuna bambancin yare, yanki ko addini ba. Saboda haka tallafin bai tsaya sai ya dan PDP ba, hakki ne ga kowane dan asalin mazabar Bade/Jakusko.”

By Editor