Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya samar da hanyar jin ƙai ga ɗalibai 66 ‘yan asalin Jihar Zamfara da aka dawo da su gida daga Sudan.
Gwamnatin Jihar Zamfara ce ta tura Ɗalibai 66 karatu Sudan, waɗanda kuma ba su kammala karatunsu ba aka dawo da su sakamakon yaƙin da ya kaure.
A wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa Kwamishinan Ilimi ne ya yi ƙarin haske ga Majalisar Zartaswar Jihar Zamfara a zamanta na ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Ya ƙara da cewa, ɗalibai 14 cikin 66 da aka dawo da su daga Ƙasar ta Sudan suna gab da rubuta jarabawar ƙarshe a fannin Jinya, kafin farawar yaƙin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A watan da ya gabata ne Gwamna Dauda Lawal ya bayar da umurni ga Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Zamfara da ta ƙulla yarjejeniya da hukumar gudanarwar Jami’ar Sudan domin ganin ɗalibai 14 ‘yan salin Zamfara sun iya rubuta jarabawarsu ta ƙarshe a Nijeriya. Wanda a tsarin jami’ar ta Sudan, Nijeriya ba ta daga cikin cibiyoyin da za a iya yin wannan jarabawa a faɗin duniya. Amma bisa jajircewa irin ta gwamnatin Zamfara ya sa suka aminta.
“Haka kuma Gwamnatin ta Zamfara ta roƙi Jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto da ta bada Asibitin Ƙwararru na Jami’ar domin a gudanar da wannan jarabawa. Wanda kuma Jami’ar ta Dan Fodio ta amince.
“Cikin tausayawa da jin ƙai irin na Gwamna Dauda Lawal ne ya ɗauke nauyin kuɗin jirgi, masauki da duk wata ɗawainiya ta malamai uku da suka zo Nijeriya daga Sudan don gudanar da wannan jarabawa. Wannan kuwa duk na daga cikin irin kishin da gwamnan yake da shi ga harkar ilimi ne.
“An gudanar da wannan jarabawar ne ga ɗaliban Zamfara 14 daga ranar 23 ga watan Satumba zuwa 30 ga watan Satumbar 2023.
“Gwamnatin ta Zamfara tana ci gaba da bin duk matakan da suka dace don ganin an kammala samar da guraben karatu ga ragowar ɗalibai 52 da suka dawo.
“Tuni Ma’aikatar Ilimi ta Zamfara ta kammala ɗaukar bayanan ɗalibai 32 cikin 52 da suka rage, waɗanda suka kammala duk wata tantancewa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya dake Abuja.
“Da zaran Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta kammala tantance ɗaliban, za a samar musu da guraben karatu a mabambantan jami’o’i.”
