Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A duk shekara, Majalisar Ɗinkin Duniya tana ware ranar 5 ga watan Oktoba, domin ta zama ranar da duniya za ta tuna da gudunmawar da malamai ke bayarwa wajen yaƙi da jahilci, koyar da ilimi ga yara masu tasowa da kuma horar da matasa da sauran masu nazari da bincike kan fannonin rayuwa daban-daban, domin su samu ƙarin ilimi da gogewa.
Tun daga shekarar 1994 da aka fara tsayar da wannan rana duniya ke bukin ranar, wajen tattaunawa da nazarin yadda gwagwarmayar malamai da sadaukarwar su take samar da ilimi mai inganci, da ɗora al’umma a tafarkin cigaba ta hanyar wayar da kai da nuna musu abubuwan da suka kamata da waɗanda ba su dace ba, wanda rayuwa za ta inganta da su.
A wani sakamakon bincike da Hukumar UNESCO mai kula da harkokin ilimi, binciken kimiyya da fasaha da rayuwar qananan yara, da ke qarqashin Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar an yi nuni da cewa, akwai yara kimanin miliyan 4 da dubu ɗari 5 da ke rayuwa a ƙasashen Afirka na kudu da Sahara, waɗanda ba su samu damar zuwa makaranta ba. Yayin da misalin kashi 52 cikin ɗari na yara mata a duniya ba sa samun damar shiga makaranta.
Ƙudiri na 4 na jerin ƙudirori 17 don samar da ingancin rayuwa a duniya, wanda shirin SDG na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tsara da nufin cimma su nan da shekarar 2030, an sanya samar da ingantaccen ilimi a jerin muhimman abubuwan da za su samar wa ɗan Adam cigaba da inganta rayuwar sa. Daga cikin matakai 10 da aka yi la’akari da su a matsayin ginshiƙin cimma nasarar samar da ingantaccen ilimi akwai batun samar da ƙwararrun malamai da kyautata rayuwarsu ta hanyar samar musu da muhallin koyarwa mai kyau, kayayyakin karatu, albashi mai kyau da tura su samun horo da ƙaro ilimi a kai a kai.
Amma anya kuwa malamai suna samun wannan kulawa da gatan da ya kamata, ba ma a Nijeriya kaɗai ba har ma da duniya baki ɗaya? Malamai na da matuƙar muhimmanci da tasiri a kowacce al’umma, amma ba kasafai ake kula da wannan martaba ta su ba. Sun kasance na bayan baya a jerin ma’aikata da ake ganin su da kima, a idon jama’a. Darajar aikin koyarwa kullum sai ƙara faɗuwa take yi, saboda yadda gwamnati da hukumomi ke yi wa harkar ilimi riƙon sakainar kashi.
A ƙasashen Afrika irin Nijeriya aikin koyarwa ya zama aiki mafi ƙasƙanci da duk wanda ya rasa aikin yi, sai ya shiga koyarwa a matsayin aikin mara aikin yi. Saboda rashin mutunci da martabar da ake yi wa masu aikin koyarwa. Masu makarantu waɗanda wasun su su ma da malamai ne, ba sa biyan malaman da ke koyarwa a ƙarƙashin su haƙƙoƙin su a kan lokaci, ko kuma biyan su wani abin kirki da zai rufa musu asiri, su da iyalan su. Wannan matsala ba ta tsaya ga makarantu masu zaman kansu kaɗai ba har ma da na gwamnati.
Malamai da dama a Nijeriya na ganin idan har wannan alƙawari na gwamnati ya tabbata to, malamai a ƙasar nan za su ji daɗi, kuma kima da martabar su za ta dawo a idon jama’a, ta yadda sai wane da wane ne zai iya samun damar shiga aikin koyarwa. Amma kuma wanne canji hakan zai yi ga harkar koyarwa? Da inganta albashin sauran malamai da ke ƙarƙashin makarantu masu zaman kansu? Idan aka lura yanzu, musamman a birane makarantun gwamnati sun zama kufayi, sai ’yan ƙalilan ne suke da tasiri, inda za ka ga ɗalibai da malamai ana karantarwa. Domin kuwa akasarin iyaye sun fi sanya ’ya’yansu a makarantun kuɗi ko na masu zaman kansu, don suna ganin nan ne yaransu za su samu koyarwa mai inganci.
Wani ƙarin ƙalubalen kuma shi ne na rashin samun gogewa a harkar koyarwa, domin kuwa ba duka malamai ne da ke makarantu masu zaman kansu suke da shaidar karatu ta NCE ba, wato shaidar da ke tabbatar da sun samu ƙwarewa ta musamman a harkar koyarwa. Ko da yake jihohi da dama sun fara wannan yunƙuri na tantance malamai, da tabbatar da ingancin ƙwarewar su, amma akwai buƙatar ko bayan samun takardun shaidar karatu, a kuma ƙara mayar da hankali wajen ƙara horar da malamai muhimman dabarun koyarwa na zamani, domin su fahimci sabbin hanyoyin koyar da ilimi.
Ga batun matsalolin tsaro da suka tarwatsa iyalai da dama da mayar da wasu makarantun sansanonin ‘yan gudun Hijira. Ga qalubalen ’yan bindiga da ’yan ta’adda da ke far wa makarantu suna sace ɗalibai suna garkuwa da su, don neman kuɗin fansa, abin da ke ƙara tsoratar da iyayen yara tura yaransu makarantun kwana ko waɗanda ke nesa da gida.
Ko a kwanakin nan ma sai da wata ƙungiyar ’yan ta’adda da ake ganin suna da nasaba da qungiyoyin fulani masu ɗauke da makami sun sace ɗalibai biyar a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin Ma a Jihar Katsina, qasa da wata guda da sace wasu ɗalibai 24 da wasu mazauna yankin Sabon Gida da ke Gusau a Jihar Zamfara. Wannan irin barazana ba a kan ɗalibai kaɗai ta tsaya ba, har ma da malaman su, waɗanda sau da dama da su ake haɗawa a sace, a duk lokacin da ’yan bindiga suka kai farmaki wata makaranta, da niyyar ɗiban ɗalibai.
A cikin saƙonsa ga ’yan Nijeriya albarkacin wannan rana ta malamai ta 2023, shugaban qasa Bola Ahmed Tinubu ya koka da halin da ya ce malamai na fuskanta na rashin kyan yanayin muhallin aiki, cinkoson ɗalibai a ajujuwa, da rashin samun damar zuwa ƙarin karatu, sakamakon watsi da harkar koyarwa da gwamnati ke yi a baya. Yayin da ya yi alƙawarin samar da kyakkyawan tsari da albashi mai kyau ga malamai a ƙasar nan.
Ya ce, in ba tare da ƙarfafa gwiwar malamai da inganta rayuwarsu ba, ba za a cimma nasara a gyaran da ake so a yi wa harkar ilimi a kasar nan ba. Ya kuma yi wa malamai albishir ɗin cewa, gwamnatin tarayya ta amince a haɗe dokar shekarun ritayar malami a Nijeriya ta shekarar 2022 zuwa shekara 40 ko kuma idan malami ya cika shekaru 65 a duniya.
A wannan shekara, bukin ranar ya mayar da hankali wajen duba irin malaman da suka dace da tsarin ilimin da ake so. Taken da za a iya cewa ya zo a daidai lokacin da rayuwar ake samun sauye-sauye a harkar ilimi da ilimantarwa a duniya, tun bayan ɓullar annobar Korona, da kuma cigaban da ake daɗa samu ta fuskar kimiyya da fasaha.
Muna fatan gwamnatin tarayya za ta cika alƙawarin da ta yi wa malamai na fara ganin sauyi a albashinsu, da yanayin yadda suke gudanar da ayyukansu. Kuma mu ga gwamnatocin jihohi su ma sun yi koyi da haka, ba tare da ɗaukar dogon lokaci ba. Har wa yau da fatan su ma malamai za su yi amfani da wannan damar wajen qara kyautata ayyukansu, da inganta ilimin su na koyarwa, bisa sabbin tsare tsaren koyarwa na duniya, kamar yadda taken bikin ranar na bana ke ƙarfafawa.
