Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce, kashe ’yan bindiga fiye da 100 a Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Wannan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya umarci dakarun su bi ’yan bindigar har mavoyar su don kawar da su.
Rahotanni sun ce sashin sojin sama na rundunar Operation Hadarin Daji ce ta yi wannan aiki, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa yan bindigar suna kan hanyar su ta kai hari a wani ƙauye.
Majiya daga rundunar sojin ta ce, dakarun rundunar sun yi amfani da jirgin sama wajen kashe yan bindigar da ke tafiya cikin ayari da mashinan su, a yankin Dansadau na ƙaramar hukumar Maru.
Akwai kuma raunata wasu ’yan bindigar da dama a yayin arangamar da suka yi da sojojin Nijeriya.
Wannan na zuwa ne ƙasa da kwana guda bayan da babban hafsan sojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya umarci dakarun nasa su gaggauta kawar da ’yan bindigar da ke addabar al’ummar ƙasar, musamman a jihohin Arewa Maso Yamma.
A lokacin wata ziyara da ya kai wa dakarun rundunar sojin Nijeriya da ke yaki da ƙungiyar Boko Haram ne Janar Christopher Musa ya umarci dakarun su daina jira sai yan bindigar da sauran masu ɗauke da makamai sun kawo masu hari kafin su dauki mataki, inda ya bayar da umarnin bin masu laifin har mafakar su domin kawar da su.
“Kada ku kwanta a sansaninku kuna jira su zo, ku tabbata kun zaƙulo maƙiya da ke addabar mutanen mu ku kashe su. Abin da ya fi dacewa shi ne ku same su har maɓoyar su, kuma ku kawar da su’’ inji Janar Musa.
A lokacin ziyarar dai babban hafsan tsaron Nijeriya ya isar da saƙon shugaban ƙasar, Bola Tinubu wanda ya ce yana sane da sadaukarwar da dakarun sojin ke yi wajen yaƙi da yan bindiga da sauran masu tayar da ƙayar baya, da kuma neman zaunar da ƙasar lafiya.
