Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai kira taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya ba kwanaki 44 da kammala zaman majalisar da aka gudanar a ranar 28 ga watan Agusta.
Hakan ya cigaba da haifar da ayar tambaya kan ko hakan na iya shafar harkokin mulki ko a’a?
Majalisar Zartaswa ta Tarayya, wadda shugaban ƙasa ke jagoranta, ita ce Majalisar Zartarwa ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya kuma wani ɓangare na zartarwa.
Matsayin tsarin mulki na FEC, kamar yadda yake ƙunshe a cikin Dokar Ayyuka na Ministoci, ita ce ta zama ƙungiya mai ba da shawara ga shugaban ƙasa.
A ranar 21 ga watan Agusta ne shugaba Tinubu ya rantsar tare da ƙaddamar da ministoci 45 da suka halarci taron majalisar ministocin da aka yi a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar 28 ga watan Agusta.
Shugaban ya kwashe kwanaki 20 yana jinya a watan Satumba kaɗai. Ya shafe kwanaki takwas yana halartar taron G20 a New Delhi, Indiya, kuma ya yi tattaunawa a Abu Dhabi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), don tattaunawa ta gaba don magance takamammen batutuwa masu muhimmanci a cikin dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, bayyana tattaunawar, jakadan UAE ya kai masa ziyara a fadar gwamnati da ke Abuja.
Kwanaki 12, shi ma a watan Satumba, ya yi tafiya zuwa babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a birnin New York na ƙasar Amurka, da sauran fita.
