Tinubu ya cire FCT daga tsarin Asusun Bai-ɗaya, ya ƙarfafa Wike kan tara kuɗin shiga

Spread the love

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya cire Hukumar Birnin Tarayya FCTA daga tsarin Asusun Bai-ɗaya (TSA).

Shugaban ya ce ɗaukar wannan mataki zai ƙarfafa wa Ministan Abuja, Nyesom Wike wajen sarrafa kuɗin shigar da Abuja ke tarawa yadda ya kamata wajen bunƙasa birnin.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma’a, Wike ya ce Tinubu ya amince da ƙirƙiro Hukumar Kula da Ma’aikata ta Abuja.

Ya ce yin haka zai bada damar cigaban ma’aikatan FCT.

Kafin wannan lokaci ma’aikatan yankin Abuja na kokawa kan rashin wannan hukuma wadda za ta kula musu da cigabansu a bakin aiki.

By Editor