Ya binne ƙaninsa da ransa kan satar Naira 1,000 a Kogi

Manhaja logo
Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Larabar da ta gabata ne al’ummar Apamisede da ke Ƙaramar Hukumar Adavi ta Jihar Kogi suka shiga ruɗani yayin da aka binne wani yaro ɗan shekara takwas da ransa sakamakon satar kuɗi naira dubu ɗaya kacal (N1000) mallakin mahaifiyarsa.

A cewar shaidar gani da ido, mahaifiyar yaron ta umurci babban ɗanta mai shekaru 19 da ya hukunta yaron saboda satar kudin.

Babban yaya wajen aiwatar da umarnin mahaifiyarsa, ya yanke shawarar binne yaron da ransa har sai da makwabta nagari suka kawo masa ɗauki suka tono yaron da ke numfashi da ƙyar.

Jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sandan (PPRO), William Ayah, ya ce an kama yaron kuma ana ci gaba da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.

By Editor