Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani fasto mai shekara 61 ya bayyana a kotun da ke sauraren ƙararrakin cin zarafin mata da yara ƙanana a Ikeja da ke Jihar Legas cewa, Mista Godwin Emmanuel, wanda yake haya a gidansa, ya yi wa ‘yarsa mai shekara 16 fyaɗe kuma har ya firka ma ta ciki.
Ɓangaren da ya shigar da ƙarar ya bayyana cewa, Emmanuel ya yi wa yarinyar fyaɗe a watan Afrilu da Yuni 2021 a gidan da yake yin haya a Ajangbadi dake Badagry.
Sai dai kuma Emmanuel ya musanta laifin da ake zarginsa da shi.
Faston ya bayyana a kotun cewa Emmanuel ya fara haya a gidansa shekaru 3 zuwa 4 da suka wuce kuma ita ‘yar tasa da kanta ta bayyana cewa shine ne ya ɗirka mata cikin.
“Na sanar da ofishin ‘yan sandan Area K dake Badagry sai dai basu ɗauki mataki a kai ba, daga nan ne na sanar wa cibiyar dake bibiyar ƙararrakin cin zarafin mata da yara ƙanana.
Ya ce ‘yarsa ta bayyana cewa matar Emmanuel ta bata wasu ƙwayoyi domin cikin ya zuba amma sai bai zube ba ta haifi ‘ya mace.
“Ɗiya ta ta faɗi min cewa wata rana yayin da suke saduwa sai kororo roban da ɗan hayan ya saka ya fashe, bayan sun gama sai Emmanuel bayan ya tabbatar tana da ciki sai ya shawarce ta ta ce wani ne ya yi mata ba shi ba.
Alqalin kotun Abiola Soladoye ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 12 ga Disemba.
