Mataimakin Gwamnan Kebbi ya yi kira a ƙara ƙaimin tsaro kan iyakoki

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Mataimakin Gwaman jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi ya yi kira ga hukumar kula da kan iyakokin Nijeriya da su ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro kan iyakokin.

Ya yi wannan kiran a garin Sakkwato ranar Talatar da ta gabata a wajen wani taron ƙara wa juna sani da aka shirya don daƙile ayyukan ta’addanci a kan iyakokin ƙasashen da jihohin da ke maƙotaka da Nijeriya.

Sanata Umar Tafida wanda shi ne ya jagoranaci shi rin ya ce ba shakka ƙirƙiro wannan kwamiti zai zaƙulo hanyoyin samar da tsaro da  zai taimaka wajen magance rashin tsaro kuma zai wanzar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin dake zaune kan iyakokin.

Ya bayyana cewa jihar Kebbi tana aiki tare hukumar kula da iyakokin Nijeriya da ke vangaren ta wajen wanzar da zaman lafiya da kuma hulɗar cinikayya mai kyau da ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Benin da ke makotaka da ita.

Daga ƙarshe an shirya wani ƙudurin haɗa hannu tsakanin hukumar kula da iyakokin Nijeriya da gwamnaticin jihohin da ke maƙotaka da waɗansu ƙasashe da kuma jami’an tsaro da sarakunan gargajiya don aiki tare wanda zai samar da tsaro da kuma zaman lafiya mai ɗorewa  da yaƙi da ta’addanci da ke faruwa kan iyakokin.

Taron ya samu halartar mataimakan gwamnonin jihohin Kebbi, Alhaji Idris Muhammadu Gobir na Sakkwato, Alhaji Faruku Lawal na  Katsina da Injiniya Aminu Usman daga Jigawasai wakilai daga jihohin Zamfara da Borno da kuma Yobe da jami’ai daga hukuma Mai kulawa da iyakokin Nijeriya da kuma shugabannin ƙananan hukumomin Arewa, Augie, Dandi,  da sarakunan gargajiya da ke kan iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.