Ƙarancin kuɗi: Ƙarin albashin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya haɗu da tsaiko

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ana ƙara nuna damuwa kan yadda batun alƙawarin Gwamnatin Tarayya na ƙara wa ma’aikatanta albashin Naira 35,000 na tsawon watanni shida ke fuskantar ƙalubalen kuɗi.

Bincike ya nuna cewa, Gwamnatin Tarayya ba ta da isassun kuɗaɗe da za ta cika alƙawarin da ta ɗauka na ƙara wa dukkan ma’aikatan tarayya albashi, alƙawarin da ta ɗauka a lokacin da aka cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.

A lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da Ƙungiyoyin Kwadago ta Nijeriya NLC da TUC a ranar 2 ga watan Oktoba na wannan shekara, ya amince da bayar da Naira 35,000 ga kowane ma’aikacin Gwamnatin Tarayya a ƙoƙarin rage tasirin cire tallafin.

Yayin da ma’aikata ke maraba da sanarwar, ƙungiyar ta NLC ta nuna jin daɗin ta game da karramawar da fadar shugaban ƙasa ta bayar.

Sai dai duk da hasashen da ake yi na ƙarin albashi daga baitul malin Gwamnatin Tarayya, gwamnati ba ta da isassun kuɗaɗen da za ta biya dukkan ma’aikatanta. An sanar da wannan ƙarancin kuɗi ga hukumomin gwamnati, waɗanda aka umarce su da su samo nasu kuɗaɗen su biya ma’aikatansu maimakon dogaro da asusun tarayya.