Daga BASHIR ISAH
Wata ƙungiya ta mabobin Jam’iyyar ANPP tare da tawagar masu ruwa da tsaki sun buƙaci ‘yan Nijeriya da su bai wa Shugaba Bola Ahmad Tinubu da gwamnatinsa cikakken goyon baya don cigaban ƙasa.
Ƙungiyar ta buƙaci hakan ne cikin sanarwar da ta fitar a Abuja mai ɗauke da sa-hannun shugabanta, Malam Kabiru Muhammad Gwangwazo.
Da yake tsokaci kan nasarar da Tinubu ya samu a Kotun Ƙoli, Muhammad wanda tsohon shugaban ANPP ne a Jihar Kano, ya yi kira ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki da su rufa wa Tinubu da gwamnatinsa baya don amfanin ƙasa.
Ya ce, “Nasarar ta tabbatar da abin da galibin ‘yan Nijeriya suka zaɓa a zaɓe mafi sahihanci wanda ya gudana a watan Fabrairu.”
Ya ƙara da cewa, nasarar da Tinubu ya samu za ta ƙarfafa ajandar sabon fata da ya gabatar wa ‘yan Nijeriya.
“Da yardar Allah nasarar alama ce ta cikar mafarkin Shugaban Ƙasa na tafiya da kowa a mulkinsa, tsarin da ‘yan Nijeriya ba su taɓa gani ba tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999 sai a wannan karo,” in ji shi.
