Daga BASHIR ISAH
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) da ta ‘yan kasuwa (TUC) sun tsunduma yajin aikin gamagari a ranar Talata.
Shiga yajin aikin na da nasaba da uƙubar da aka gana wa shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero kwanan nan a Jihar Imo, wanda a cewar ƙungiyar hukumomin da lamarin ya sha sun gaza yin komai kan batun.
Daga cikin buƙatun da NLC ta nema dangane da haka, har da neman a hukunta da kuma sallamar jami’in ɗan sandan da ya jagoranci lakaɗa wa Ajaero duka.
Haka nan, ta nemi a hukunta wani hadimin Gwamna Hope Uzodinma na yin sakaci da aikinsa da har ya bari hakan ta faru.
Ƙungiyar ta yi barazanar muddin aka gaza biya mata buƙatun da ta gindaya game da batun gana wa shugabanta na ƙasa uƙuba, ba makawa za ta tsunduma yajin aikin gamagari a ranar 14 ga Nuwamba (yau Talata).
A hannu guda, domin hana ruwan NLC gudu ya sa Gwamnatin Tarayya ta garzaya Kotun Ma’aikata a ranar Juma’ar da ta gabata, inda kotun ta bai wa NLC umarni a kan ta dakatar da shirinta na shiga yajin aiki.
Sai dai duk da umarnin kotun, hakan bai hana NLC shiga yajin aikin ba kamar yadda ta sha alwashi tun farko.
