Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An aika da jerin sunayen alƙalai 22 na Kotun Ɗaukaka Ƙara da Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Tarayya, FJSC, ta miqa sunayensu domin ɗaukaka darajarsu zuwa Kotun Ƙoli ga majalisar shari’a ta ƙasa, NJC.
Blueprint Manhaja ta ruwaito sunayen waɗanda aka naɗa, waɗanda suka fito daga yankuna daban-daban na ƙasar, an bayyanasu a cikin takardar FJSC a ranar Alhamis.
Yankin Arewa ta Tsakiya yana da mutum shida da aka zaɓa, yayin da shiyyar Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu ke da mutum biyu kowanne. Shi ma yankin Kudu maso Gabas yana da mutum shida, sannan kuma yankin Arewa maso Gabas yana da mutum biyu.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan murabus ɗin alƙalai Amina Augie da Mohammed Dattijo wanda ya bar Kotun Ƙoli da alƙalai 10 kacal.
Ga jerin sunayen alƙalan da aka zaɓa:
Kudu maso Gabas:
Hon Justice Nwaoma Uwa (Jihar Abiya); Hon Justice Onyekachi Otisi (Jihar Abiya); Hon Justice Obande Ogbuinya (Jihar Ebonyi); Hon Justice Theresa Orji-Abadua (Jihar Imo) Hon Justice Anthony Ogakwu (jihar Enugu) da Hon Justice Chioma Nwosu-lheme (Jihar Imo)
Kudu maso Kudu:
Hon Justice Moore Adumein (Jihar Bayelsa); Hon Justice Biobele Georgewill (Jihar Ribas)
Kudu maso Yamma:
Hon Justice Adewale Abiru (Legas); Hon Justice Olubunmi Oyewole (Jihar Osun).
Arewa ta Tsakiya:
Hon Jummai Sankey (Jihar Filato); Hon Justice Muhammad Ibrahim Sirajo (Filato); Hon Justice Stephen Adah (Jihar Kogi) da Hon Justice Ridman Maiwada Abdullahi (Jihar Nasarawa); Hon Justice Baba Idris (Jihar Neja) da Hon Justice Joseph Ikyegh (Jihar Benue).
Arewa maso Gabas:
Hon Justice Haruna Simon Tsammani (Jihar Bauchi); Hon Justice Abubakar Talba (Adamawa)
Arewa maso Yamma:
Hon Justice Muhammad Lawal Shuaibu (Jihar Jigawa); Hon Justice Bello Aliyu (Zamfara); Hon Justice Abubakar Sadiq Umar (Jihar Kebbi); Hon Justice Abdullahi Mahmud Bayero (Kano).
