Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buƙaci Bankin Bunƙasa Afirka (AfDB) da ya saka Jihar Zamfara cikin shirinsa na taimaka wa shiyyoyin harkokin noma (SAPZ) kashi na biyu.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron da gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma suka yi da Shugaban AfDB, Dr. Akinwunmi Adesina a ranar Asabar.
SAPZ shiri ne mai manufar daƙile fitar kayan gona zuwa ƙetare, maimakon haka ya zamana ana sarrafa su a cikin gida.
Sanarwar da Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, Zamfara ba ta samu shiga kashin farko na shirin SAPZ ba a 2021 amma za ta ci gajiyar shirin kashi na biyu bayan da Gwamnan ya sa baki a lamarin.
A cewar sanarwar, jihohin Arewa maso Yamma ciki har da Zamfara, za su fuskanci cigaba a ɓangaren noma, wanda hakan babbar gudunmawa ce ga cigaban tattalin arzikin Nijeriya.
Ya ce, “Taron da aka yi tsakanin Gwamnonin Arewa maso Yamma da Dr. Akinwumi Adesina, Shugaban Bankin Bunƙasa Afirka, ta buɗe ƙofofin damammaki ga jihohi bakwai da yankin ya ƙunsa.
“Gwamnonin Zamfara, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Kano da kuma Kaduna sun sanar da Shugaban AfDB game da muhimman wuraren da ke shiyyar da ke buƙatar a ba su muhimmanci.
“Gwamnonin sun nemi taimakon Bankin domin magance ƙalubalan da jihohinsu ke fuskanta, irin su matsalar tsaro, harkokin noma da sauransu. Waɗannan muhimman ɓangarori ɗamfare suke da juna kuma masu matuƙar tasiri ga cigaban al’umma.
“Ta hanyar haɗa hannu da kuma jagorancin AfDB, Gwamnonin Arewa maso Yamma za su inganta al’ummominsu. Ba ma jawo hankali masu zuba jari kaɗai ba, hakan zai taimaka wajen samun cigaba mai ɗorewa ga tattalin arziki,” in ji Gwamna Dauda.

A nasa ɓangaren AfDB ya bayyana aniyarsa ta tallafa wa shiyyar Arewa maso Yamma ta Nijeriya don ta bunƙasa.
Kazalika, Shugaban Bankin ya yaba da yadda gwamnonin suke bai wa walwalar al’ummominsu muhimmanci.
