Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ƙungiyar masu fama da ciwon siga ta Nijeriya ta ce aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 11.2 ne ke ɗauke da cutar a halin yanzu.
Dr Alƙali Mohammed, shugaban ƙungiyar ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a wani taron zagayowar ranar tunawa da cutar siga ta duniya ta 2023, WDD.
WDD rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta keɓe domin jawo hankalin jama’a kan buƙatar ɗaukar matakan yaƙi da cutar.
Taken bikin ranar na bana shine, “Samun kula ga masu ciwon siga.”
Mohammed ya bayyana cewa daga cikin ‘yan Nijeriya miliyan 11.2 da ke fama da ciwon siga, kashi 90 cikin 100 na ɗauke da nau’i na 2 na ciwon ciwon, inda ya ce cutar na iya shafar kowane vangare na jiki.
Ya kuma bayyana cewa kimanin mutane miliyan 537 ne aka rubuta suna ɗauke da cutar a faɗin duniya.
Ya ƙara da cewa, an yi hasashen adadin zai iya ƙaruwa zuwa miliyan 737 nan da shekarar 2040 idan ba a yi wani abu don daƙile cutar ba.
Mohammed, ya bayar da shawarar ƙara haraji kan kayayyakin shaye-shaye masu zaqi, SSBs, daga kashi 10 cikin 100 zuwa 20, yana mai cewa harajin zai inganta al’adun kiwon lafiya da muhalli ta hanyar hana shan kayan zaƙin barkatai.
