Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Hassan Garban Ƙauye Farawa ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai guda 60 ‘yan asalin yankin a Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi dake jihar Kano.
Ya ce ɗaliban da aka ɗauki nauyin karatun nasu wani sauke nauyi ne da Allah ya ɗora masa da wajibi ne ya yi iya ƙoƙarinsa domin sauke nauyin.
Ya taya ɗaliban da suka rabauta murna da jan hankalinsu akan su dage da karatu yanda zai amfanesu su kuma jakadu nagari ga ƙaramar hukumar Kumbotso a jami’ar domin duk abinda suka yi za a kalli ‘yan Kumbotso ne suka yi.
Alhaji Hassan Garban Ƙauye ya shaida wa ɗaliban duk cikarsu har su kammala jami’ar ba wanda zai biya kuɗin makaranta an biya musu gaba ɗaya.
Ya qara da cewa irin wannan ɗaliban suna da na kason farko da na biyu da dama aka biya musu suna karatu a jami’ar. Akwai ma wasu ɗaliban a makarantar Tarathu da aka biya musu har ma sun kammala karatun, sannan akwai ɗalibai a makarantar fasahar lafiya ta Bichi suma kaso na farko dana biyu har wasu sun gama an yayesu suna bada gudummuwa na kula da lafiya a unguwanninsu kafin su sami damar samun aiki.
Hon. Hassan Garban Ƙauye ya ce a cikin ɗaliban na lafiya da suka kammala zai tallawa kowanne ɗaya da magunguna na N100,000 don su riqa kula da lafiyar al’ummarsu a unguwanni da suke a zaune.
