Za mu haɗa kai da sarakunan gargajiya domin daƙile matsalar tsaro – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, a ƙarshen mako ya ce gwamnatinsa za ta haɗa kai da sarakunan ƙasar nan domin tabbatar da ci gaba da kawo ƙarshen rashin tsaro.

Tinubu ya bayyana haka ne a yayin bikin cika shekaru 70 da haihuwar Osemawe na masarautar Ondo, Oba Victor Kiladejo, wanda aka gudanar a Cocin Diocese of Ondo (Anglican Communion) Cathedral Church na St. Stephen a cikin birnin Ondo.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Ministan Harkokin Cikin Gida, Mista Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce haɗin gwiwar ya zama wajibi domin zaman lafiya da kwanciyar hankali su karaɗe faɗin ƙasar nan.

Ya kuma buƙaci sarakunan da su ba gwamnatinsa haɗin kai, ya ƙara da cewa ribar dimokuraɗiyya za ta zagaya ko’ina.

Da yake tsokaci game da mulkin Oba Koladejo na shekaru 17 da suka wuce, wanda ya bayyana zaman lafiya, Tinubu ya ce, a bayyane yake cewa shekaru 17 da suka wuce, mai martaba sarki ya sanya wannan babban ofishin ya zama abin sha’awa ga kowa.

“A yau, babu wanda ya isa ya wuce gona da iri domin ganin irin tasirin da mulkinka ya yi akan al’ummar Ondo Ekimogun. Ana ganinsu a ko’ina cikin al’umma, kuma suna shafar dukkan ɓangarorin ɗan Adam.”

Oba Kiladejo, wanda ya yaba wa Tinubu bisa karrama shi da cika shekaru 70 a duniya, da kuma cika shekaru 17 a kan karagar mulki, ya yaba wa shugaban ƙasar kan naɗa Tunji-Ojo a matsayin ɗaya daga cikin ministocinsa.