Daga AISHA ASAS
Daga ƙarshe dai fitacciyar mawakiyar Colombia, Shakira ta cimma yarjejeniya da masu shigar da ƙara na Ƙasar Sifaniya kan sasantawa dangane da tuhumar almundahanar biyan haraji da ke kanta. Yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin fara zaman kotu da ita.
Mawakiyar ta biya tarar Yuro miliyan 7.5m, duk da cewa, a buƙatar masu gabatar da ƙara a yanzu sun so a ɗaure ta tsawon shekara takwas, sannan a ci ta tarar Yuro miliyan 23.8, idan aka same ta da laifi.
Kamar yadda Blueprint Manhaja ta ruwaito maku a ‘yan watannin baya, mawaƙiyar ta fuskanci zargin almundahana kan kuɗi Yuro miliyan 14.5 a wata kotun Barcelona.
Duk da cewa, mawaƙiya Shakira, ta sha musanta aikata ababen da ake tuhumar ta da su, sai dai ta bayyana cewa, wannan ma ba wai amincewa da yarjejeniyar na nufin ta amsa laifukan da ake tuhumar ta da su ba, sai dai ta yarda da yin hakan ne don ‘ya’yanta.
A cikin wani dogon bayani da ta yi, ta bayyana cewa, ‘ya’yanta ba sa son ganin mahaifiyarsu ta yi wasa da rayuwarta akan wani rikici, don haka duk da cewa, a baya ta yi watsi da yarjejeniyar wadda masu gabatar da qara suka kawo mata a matsayin maslaha, ta nemi a je kotun can ayi ta ta ƙare, sai dai albarkacin ‘ya’yan nata, ta haƙura, ta karvi yarjejeniyar gabanin shiga kotun.
Idan ba ku manta ba, a ‘yan watannin baya mun kawo maku rahoto kan yadda rikicin ya soma, inda muka ce, rikici ne da ya shafi ƙasar da mawaqiyar ta ke zaune tsakanin shekarar 2012 zuwa 2014, inda masu gabatar da ƙara suka tuhume ta da lissafa zaman wannan lokacin da ta yi a wani wuri, alhali a dokar Ƙasar Sifaniya matuƙar ka shafe fiye wata shida a qƙasar, to haƙoƙƙin gwamnati kan jama’arta ta fuskar biyan haraji zai hau kanka.
