Liverpool tana shirin faɗaɗa Anfield kafin wasanta da Manchester United

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Liverpool na shirin buɗe saman filin wasanta na Anfield lokacin da za ta fafata da Manchester united a ranar 17 ga watan Disamba.

Wannan dai na cikin wani shiri na faɗaɗa filin da ta ke yi daga mai ɗaukar mutum 7,000 zuwa 61,000, wanda zai ci maau kallo miliyan 80.

Ana cewa aikin zai samu tsaiko zuwa 2024, bayan ƙungiyar ta sauya kwataragi da kamfanin da za su yi aikin.

Amma Liverpool ta ce shirin buɗe filin wasan gabanin wasanta da Manchester na ƙila-wa-ƙala, domin sai masana sun yi nazari kai, saboda kare rayuwar ‘yan kallo.

Aikin zai shafi wasan da ƙungiyar za ta fafata da West Ham da Arsenal da Newcastle a ƙarshen watan Disamba.

An tsara kammala aikin gabanin fara kakar 2023-2024.

Amma ya zuwa yanzu ƙasan filin wasan kawai aka iya buɗewa ga magoya baya a wannan kakar, wanda aka samu mazaunai da suka kai 50,000.