Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙalubalanci Obasanjo kan kalamansa ga dimukraɗiyyar Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo kan halin da dimokraɗiyyar Nijeriya ke ciki a halin yanzu.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Bayo Onanuga, mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, ya nuna cewa Obasanjo na da tasiri kai tsaye kan irin dimokuradiyyar da al’umma ke yi a yau.

Ya ce tasirin Obasanjo ya kai wa’adi biyu a matsayin shugaban qasa, na farko a matsayin shugaban farar hula daga 1999 zuwa 2007 sannan a matsayin shugaban qasa na soja daga 1976 zuwa 1979.

“Ya kamata Obasanjo ya san cewa shi ya kawo wannan abu cikin Nijeriya. Shi ne ya sa mu karɓe ta a 1979, tabbas akwai rashin dacewa lokacin da ya yi mulkin mu na tsawon shekaru takwas, har ma ya so a qara wa wasu shekaru huɗu.

“Don haka, yadda yake surutai, kamar mutumin yana qara wayo ne bayan ya bar ofis,” in ji Onanuga, yayin da yake mayar da martani ga matsayin Obasanjo bayan shugaban ƙasa.

Kalaman fadar shugaban ƙasar sun biyo bayan kalaman tsohon shugaban ƙasar ne a babban taron tuntuɓar dimokuraɗiyya mai sassaucin ra’ayi a Afirka, wanda aka gudanar a ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library’s Green Resort Legacy da ke Abeokuta.

Obasanjo dai ya caccaki dimokuraɗiyyar ƙasashen yammacin duniya, inda ya ce ba ta taimaka wa ci gaban Afirka da kuma shugabanci nagari ba.

Da yake bada misali da yadda tsarin yammacin Afirka ke raina tarihi da sarƙaƙiyar Afirka, ya ba da shawarar sake yin nazari da gyara tsarin dimokuraɗiyya don dacewa da ƙasashen Afirka.

Da yake gano raunin da ke cikin dimokuraɗiyya mai sassaucin ra’ayi, Obasanjo ya bayyana ta a matsayin gwamnatin mutane kaɗan a kan dukkan jama’a ko yawan jama’a kuma waɗannan mutane kaɗan wakilan wasu ne kawai kuma ba cikakkun wakilan jama’a ba ne.

Ya yi iƙirarin cewa galibin mutane ana keɓe su, ko da gangan ko kuma bisa kuskure.

By Editor