Kamfanin Boska ya raba wa masu babura hular kwano 698 a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Don ganin an rage yawan mutuwa a sanadiyar hatsari, Kamfanin Dexa da suke yi maganin nan na Boska ya raba wa mahaya babura sama da 600 hular kwano kyauta a Gombe.

Kamfanin na Boska ya yi haɗin gwiwa ne da hukumar kiyaye hatsura ta ƙasa FRSC reshen Jihar Gombe don ganin cewa suna da ruwa da tsaki wajen faɗakar da masu baburan muhimmancin sanya hular kwano ga duk mai hawa babur.

Da ya ke jawabi a lokacin raba hular kwanon Kwamishinan Ma’aikatar tsaron cikin gida na jihar Gombe Laftanal Abdullahi Bello mai ritaya, ya yaba wa kamfanin na Dexa inda ya ce lailai hular kwano na da matuƙar muhimmanci ga masu hawa babura musammam idan hatsari ya auku maimakon a samu fashewar kai wannan hular kwano tana taimakawa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan ƙoƙari na kamfanin Dexa zai isar wa gwamna domin sun ɗauki wani ɓangare daga cikin abinda gwamnati ya kamata ta yi na kare lafiyar masu baburansu suka yi.

Ya ce bai wa ‘yan acava wannan hular kwano sara ne kan gaba domin suna daga cikin mutanen da suke samarwa da jihar kuɗaɗen shiga ta hanyar biyan haraji.

Shi ma Kwamandan hukumar kiyaye haɗuran na jihar Gombe Felix Theman, cewa ya yi hular kwano tana bada kariya wajen hana fashewar kai da zarar an samu hatsari.

Felix Theman, ya ce cikin amfanin hular kwanon akwai hana ƙwari shiga idanun mai babur idan yana tuƙi wanda a sanadiyyar hakan yakan iya haifar da hatsari.

Sannan ya kiraye su da cewa su dinga tuƙi cikin nitsuwa ba tare da gudun ganganci ba inda ya ce gudun ganganci hatsari ne ga duk wani mai tuƙa abin hawa.

Mista Tony Amadi, shugaban sashin kasuwanci ta yanar gizo ya ce sun haɗa kai da hukumar kiyaye hatsuran ne suka raba wannan hular kwano saboda muhimmancin ta ga lafiyar masu tuka babur wanda ko da hatsari ya faru kai ba zai fashe ba.

Mista Tony Amadi, ya ce hular kwano 500 suka raba kuma nan gaba za su ƙara inda ya ce ko a makon da ya gabata sun gudanar da raba irin wannan hular kwana a jihar Sakkwato.

Shi ma Nnamdi Ezeani manajan shiya na kamfanin na Boska, cewa ya yi lafiya ita ce uwar jiki shi ya sa suka raba hular kwano domin taimakawa ‘yan acaɓa su kare lafiyarsu.

Sai ya ce suna son yan acaɓa su dinga saka hular kwanon ne domin ganin cewa sun kare kan su musamman a irin waɗannan watanni na Disemba na ƙarshen shekara.  

Da suke zantawa da wakillinmu wasu daga cikin ‘yan acaɓa sun bayyana cewa duk da cewa ba a tilasta sanya hulan kwano a Gombe ba amma suna gode wa kamfanin na Dexa bisa ƙoƙarinsu na samar musu da hular kwano domin kare lafiyarsu.