Tinubu ya nemi Jamus ta saka hannun jari a fannin makamashi da layin dogo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ƙasar Jamus da ta saka hannun jari a fannonin tattalin arzikin Nijeriya masu muhimmanci kamar wutar lantarki da sufurin jiragen ƙasa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale, ya fitar, ta ce Mista Tinubu ya yi wannan kiran ne a wani taro da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, a taron G20 Compact with Africa Economic Conference, ranar Litinin a Berlin.

Shugaban ya ce ana buƙatar zuba jarin Jamus a cikin muhimman masana’antu masu samar da ci gaba a fannin makamashi, sufuri, da samar da wutar lantarki, watsawa da rarrabawa.

Shugaban ya ce aiwatar da shirin samar da wutar lantarki na shugaban ƙasa da ke samun goyon bayan Siemens cikin gaggawa.

“A gare ni, na himmatu sosai wajen bin dukkan fannoni na aikin samar da wutar lantarki na Siemens da kuma damar bunƙasa fasahar da za su fito daga wannan aikin ga hazikan matasanmu waɗanda za su iya shiga cikin ci gaban masana’antar,” inji Tinubu.

Ya kuma ce kamfanin Siemens na iya taka rawa a tsarin layin dogo na Nijeriya tare da samar da jiragen ƙasa na zamani da na dogo kamar yadda ake yi a Masar, inda take gina layin dogo mai tsayin kilomita 2,000 a cikin birane 60.

Don haka, shugabar gwamnatin Jamus ta bayyana a shirye take, amma ta ce akwai buqatar a warware matsalolin harkokin mulki da na kuɗi da matsalolin shugabanci suka haifar a wannan fanni.

“Na san cewa akwai ayyuka da yawa da aka yi. Tuni dai ana samun yawaitar samar da wutar lantarki a Nijeriya, amma hakan bai kai ga yawan jama’a ba.

“Haƙiƙa, wannan yana da alaƙa da buƙatar samar da tashoshi da ababen more rayuwa.

“Siemens ta tsara shirin kuma a shirye take ta zurfafa aiwatarwa, amma yanzu ya rage ga sabuwar gwamnatinku da ta ɗauki matakin bin diddigin da kuka ƙuduri aniyar ɗauka.

“A kan shirye-shiryen layin dogo, Siemens za ta yi farin ciki sosai don yin wannan lokacin da aka sami qarin ci gaba a kan aikin wutar lantarki wanda aka riga aka fara,” inji Scholz.

Tinubu ya ja hankalin shugaban na Jamus kan buƙatar ‘yan kasuwan Jamus su mai da hankali kan sarrafa abubuwa masu amfani a ma’adanai, noma, motoci da sauran wuraren samar da ayyukan yi a Nijeriya.

“Duk wani abu da duniya ke bukata dangane da sauye-sauyen yanayin kasuwanci yana gudana  Nijeriya. Watakila masu zuba hannun jarinmu na ƙasashen waje har yanzu suna cikin rugujewar cewa waɗancan tsofaffin batutuwan Nijeriya ba za su iya magancen su ba.”