Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta yi wa yara ‘yan kasa da shekara sha biyar su fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas allurar rigakafin cutar Ƙyanda a faɗin jihar.
Babban sakatare na hukumar kiwon lafiya a mataki na farko Dr Shamsuddeen Yahaya ya faɗa wa manema labarai haka a ofishinsa.
Haka ya ce yawan yara da akai wa rigakafin a faɗin jihar ya kai kashi ɗari da uku bisa ɗari.
Dr Shamsuddeen ya kuma faɗa cewa an fara rigakafin ne a cikin watan jiya da ya ɗauki mako guda ana yi a ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jihar.
Ya bayyana cutar Ƙyanda a matsayin cuta ma bazuwa a tsakanin ƙananan yara amma nan da nan za a shawo kan cutar ta hanyar yin wannan allurar.
“Ana ɗaukar cutar ne ta hanyan iska da ake shaƙa da kuma wajen masu tari da numfashi wanda a ƙarshe akan ɗauki ciwon makanta, cimaka har ma da rasa rayuka,” ya ce.
Babban sakataren ya bayyana wannan shiri na haɗin gwiwa na tsakanin da hukumar kiwon lafiya ta qasa da da hukumar tallafa wa kiwon lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da sauran ƙungiyoyin tallafa wa harkar kiwon lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ɗan shekara 16 ya yi lalata da ƙananan yara ‘yan shekara biyar da shida a Kebbi
Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Ranar Talata 21 ga watan Nuwamba, 2023 aka kama wani matashi ɗan kimanin shekaru 16 bayan ya ruɗi waɗansu qananan yara mata biyu da ke zaune a unguwar Badariyada ke cikin garin Birnin Kebbi shalkwatar jihar ta Kebbi zuwa wani jeji da ke kusa da barikin sojoji ta Dukku inda ya yi lalata da su.
Bayanai daga hukumar Hisba sun bayyana cewa kwamiti dai ya gabatar da wanda ake tuhuma da waɗanda aka yi wa fyaɗe a gaban Ubandoma na Gwandu, inda wanda ake zargin ya amince da aikata laifin a fadar bisa raɗin kansa yayin da ake masa tambayoyi.
Binciken lafiya na farko da ma’aikacin lafiya daga Cibiyar Kiwon Lafiya ta Kebbi da ke ofishin Hisbah na fadar Ubandoma suka yi, ya tabbatar da an keta budurcin ƙananan yaran biyu.
Hakazalika gwajin ƙwayar cutuka da jami’an kiwon lafiya suka gudanar ya nuna wanda ake zargin yana ɗauke da ciwon hanta da aka fi sani da Hepatitis B. sai dai yaran basu kamu da cutar ba a sakamakon gwajin farko inda aka buƙaci ‘yan matan su maimaita gwajin bayan makonni biyu.
Yanzu haka dai bayan kammala bincinken hukumar Hisba an miqa qarar ga hedikwatar Hisbah ta jihar Kebbi inda ta hannanta maganar hannun ofishin yanki ta ‘yan sanda da ke Birnin Kebbi domin bincike da gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu.
