Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta garzaya Kotun Ƙoli domin neman a ƙara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin naira fiye da wa’adin da aka saka na ranar 31 ga watan Disamba, 2023.
Idan dai ba a manta ba, Kotun Ƙoli ta soke dokar hana amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200, 500, da 1000 a matsayin doka a farkon shekarar nan.
Dangane da haka, gwamnati na son Kotun Ƙolin ta ɗage umarnin da ta bayar na ranar 3 ga watan Maris na cewa a cigaba da amfani da tsofaffin takardun naira tare da sabbin takardun har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
Ta ƙara da cewa, ya zama dole a tsawaita wa’adin, saboda matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita, ta kasa buga adadin sabbin takardun da za ta ba ta damar cire tsofaffin kuɗaɗen kafin ranar 31 ga Disamba, 2023.
Gwamnatin Tarayya ta ƙara bayyana cewa, idan har Kotun Ƙoli ta ƙi amincewa da buƙatar da ta yi na tsawaita wa’adin buga tsofaffin takardun kuɗi, ƙasar na iya fuskantar barazanar sake faɗawa cikin wani mawuyacin hali na tattalin arziki da kuma rashin kuɗi kamar yadda aka shaida a rubu’in farko na shekarar nan. An fara aiwatar da manufar sake fasalin tsarin mulkin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele.
Gwamnatin ta qara da nuna damuwarta kan yadda tara tsofaffi da sabbin takardun kuɗi na Naira, sakamakon wa’adin da ke tafe, na iya kawo taɓarɓarewar tattalin arziki. Don hana hakan, gwamnati ta yi imanin cewa, ya kamata a cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi tare da sabbin takardun har sai an samar da matakan da suka dace don kawar da su.
Ta amince da cewa ta daɗe tana shigar da jihohi 10 masu ƙara a matsayinsu na mambobin Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC).
Jihohi goman sun haɗa da Kaduna, Kogi, Zamfara, Ondo, Ekiti, Katsina, Ogun, Kuros Rubas, Legas da Sokoto.
Waɗanda ake ƙara a ƙarar sun haɗa da babban lauyan gwamnatin tarayya, jihohin Edo da Bayelsa.
