Euro 2024: Ƙungiyoyin da suka samu gurbin shiga gasar

Daga MAHDI. MUHAMMAD

Ƙungiyoyi 20 sun samu gurbin shiga gasar Euro 22024 kai tsaye, inda Jamus za ta karɓi baƙuncin wasannin a 2024.

Ingila, wadda Gareth Southgate ke jan ragama tana cikin tawagogin da za su jira raba jadawali, bayan da ta ja ragamar rukuni na uku, itama Scotland ta samu gurbi.

Dukkan wadda ta yi ta daya da ta biyu a kowanne rukuni, su ne suka samu tikiti kai tsaye a wasannin da za a fara daga Yuni zuwa Yulin 2024.

Yanzu kenan saura gurbi uku ya rage, inda tawaga 12 za ta buga wasannin cike gurbin shiga Euro 2024.

Ƙasa 12 ce za ta barje gurbi a Euro 2024, inda Jamus da za ta karvi baƙuncin wasannin ce Kaɗai da ta samu takiti kai tsaye.

Ranar Talata aka kammala karawar cikin rukuni ta yadda aka samu 20 da suka kai Euro 2024 kai tsaye

Ƙungiyoyin da suka samu gurbin shiga gasar Euro 2024;

  • Spain
  • Scotland
  • France
  • Netherlands
  • England
  • Italy
  • Turkey
  • Croatia
  • Albania
  • Jamhuriyar Czech
  • Belgium
  • Austria
  • Hungary
  • Serbia
  • Denmark
  • Slovenia
  • Romania
  • Switzerland
  • Portugal
  • Slovakia

Yanzu kasa uku za a tantance, bayan buga karawar cike gurbi, domin samun 24 da za su fafata a Jamus a 2024.

Za a raba jadawalin cike gurbi bisa la’akari da kwazon tawaga a wasannin da suka buga a cikin rukuni.

Za a raba jadawali ranar Alhamis 23 ga watan Nuwamba, inda ake sa ran fara fafatawar a cikin farko-farkon baɗi.

Ƙungiyoyin da ke neman buga karawar cike gurbi;

  • Poland
  • Wales
  • Estonia
  • Iceland
  • Finland
  • Ukraine
  • Israel
  • Bosnia da Herzegovina
  • Georgia
  • Greece
  • Kazakhstan
  • Luxembourg

Za a raba jadawalin gasar Euro 2024 ranar Asabar 2 ga watan Disamba.