Yadda mutuwar Daraktan Kannywood, Aminu S.Bono ta girgiza al’umma 

Spread the love

*Gwamnan Kano ya girgiza da mutuwar Aminu S. Bono, inji Abba El-Mustapha
*Rasuwar Bono ta haifar da wagegen giɓi a Kannywood – Ganduje
*Zan biya ma sa bashin da ke kansa, cewar jaruma Aisha Humaira
*Jaruma Rashida Maisa’a ta ɗauki nauyin karatun ɗan marigayin
*Furodusa Kufaina ya yafe bashin da yake bin Bono

Daga AISHA ASAS 

Duk da cewa, mutuwa rigar kowa ce kuma mun amince duk mai rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa, hakan bai hana mu alhini da jimami yayin da muka rasa wani masoyinmu ba.

Duk da kasancewar mutuwa abar tayar da hankali ce a kodayaushe, kuma babu ta yadda za a yi ta kasa taɓa zukatan waɗanda aka yi wa ita ba, sai dai mutuwar fuju’a firgicinta da tashin hankalinta daban yake da na kowacce irin nauyin mutuwa, domin ta kan tava har wanda ba shi da alaƙa da mamacin matuƙar ya ji yadda mutuwar ta kasance, kuma sau da yawa ta kan zama babbar wa’azi da ke karkato da wasu kan hanya.

Da yawa akan samu masoyan mamacin da ya yi mutuwar nan take su samu firgici da zai iya tava lafiyarsu ko hankalinsu, sakamakon zuwan mutuwar a ba-zato ba tsammani. 

Daraktan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Aminu S. Bono, na daga cikin layin waɗanda suka yi irin wannan mutuwar ta nan take a cikin bazata, wanda kamar yadda Blueprint Manhaja ta ruwaito, daraktan ya rasu ne a yammacin ranar Litinin, 20 ga Nuwamba, 2023, bayan da ya yanke jiki ya faɗi a gidansa da ke Unguwar Chiranci a yankin Ɗorayi da ke Birnin Kano.

A washegari safiyar Talata ne ɗimbin ’yan fim da jama’ar gari da ’yan uwa suka halarci jana’izar marigayin daraktan kuma jarumi a masana’antar ta Kannywood, Malam Aminu S. Bono.

An yi wa mamacin sallah a gidan iyayensa da ke unguwar Ɗandago, inda daga nan aka ɗauke shi zuwa maƙabartar Ɗandolo da ke unguwar Goron Dutse, aka rufe shi a can, kamar yadda Blueprint Manhaja ta ruwaito. Daga nan aka sake koma wa gidan iyayen mamacin, don cigaba da zaman makoki.

Wannan rashi ya kaɗa ’yan fim da dama, ba ma iya su ba har da sauran jama’a, musamman ganin yadda rasuwar tasa ta yi ba-zata, babu jinya babu ko hatsari.

Tsayin lokaci kafafen sadarwa na zamani sun tsayu kan mutuwar ta yadda za ka ga kusan duk inda ka juya hotonsa ne da kuma rubutu da ake wallafawa. A iya rubutun kawai idan ka tsaya, za ka iya tabbatar da cewa mutuwar ba ƙaramin tava jama’a ta yi ba, kuma ta zaburar da wasu da tunasar da su cewa, su ma fa za ta iya riskan su a cikin yanayi na ba-zata. 

Kasancewar marigayin sananne a masana’antar finafinai ta Kannywood da ya jima yana bayar da gudunmuwa ga cigaban masana’antar, an samu manya da dama da suka nuna alhini da miqa saqon ta’aziyyarsu ga masoya da iyalan mamacin. 

Ɗaya daga cikinsu akwai Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna kaɗuwarsa bisa rasuwar fitaccen daraktan finafinan Hausa na Kannywood, Aminu S. Bono.

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne ta bakin Babban Sakataren Hukumar Tace Adabi na Jihar Kano, Abba El-Mustapha, wanda ya wakilce shi a wajen jana’aizar marigayin da aka gudanar ranar Talata, a maqabartar Ɗandolo da ke birnin Kano.

A ganawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala jana’izar, Abba ya kuma bayyana Marigayi Bono a matsayin mutumin ƙwarai mai haƙuri da sanin yakamata tare da kyakkyawar mu’amula, wanda kuma ya kai ƙololuwa wajen fiƙira a sana’arsa.

Don haka ya ƙara da cewa, al’ummar Kannywood, Jihar Kano da Nijeriya bakiɗaya sun yi matuƙar asarar rashin wannan ɗa nasu.

Daga nan sai ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, abokan sana’arsa tare da bayyana yadda gwamnatin jihar a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir ta tsuma da jin labarin rasuwar.

Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa a yanzu, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ce, rasuwar Aminu Bono ta haifar da wagegen givi a Kannywood.

Shugaban ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masa’antar finafinai da Jihar Kano da ma ƙasa bakiɗaya.

Ganduje ya bayyana kaɗuwarsa game da rasuwar marigayin, inda ya ce, mutuwar tasa ta zo a daidai lokacin da aka fi buƙatar marigayin.

Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga Ganduje, Edwin Olofu, ya sanya wa hannu, wacce aka kuma raba wa manema labarai a ranar Talata ta ce, “Bono ya yi wa takwarorinsa zarra wajen bayar da hima da kuma yaɗa al’adun Hausa/Fulani.”

Sanarwar ta qara da cewa, a halin rayuwarsa, marigayin ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen cigaban masana’antar Kannywood.

“Ina so na yi amfani da wannan lokaci wajen nuna alhini ga iyalan marigayin da ma Kannywood bakiɗaya dangane da rasuwar haziƙin darakta a masana’antar, Aminu Surajo Bono,” inji Ganduje.

Ganduje ya qara da cewa, salon rayuwar marigayin ya kyautata mutuncin Kannywood a idon waɗanda ke yi wa masana’antar wani kallo.

“Dole ne na yarda da cewa, rasuwar Aminu Surajo Bono ta haifar da wagegen giɓi a masana’antar finafinai,” a cewar Ganduje.

A ƙarshe, Ganduje ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalan mamacin da masana’antar Kannywood haƙuri da juriyar wannan rashi, kana Ya sa Aljannatul Firdausi ta zamo makomar marigayin. 

A ɓangaren abokan sana’arsa maza kuwa ba a magana, domin da yawansu sun samu halartar jana’izarsa, kuma yanayin fuskokinsu kawai za ka kalla ka san sun yi rashin da ya tava su sosai. 

Su ma matan ba su fita daban ba, domin da dama daga cikinsu sun bayyana tsananin tashin hankalinsu kan rasuwar daraktan, kamar irinsu Aisha Humaira, wacce ta wallafa faifen bidiyo, inda a cikin alhini ta bayyana mutuwar daraktan wanda ta kira shi da mutumin kirki da ko musu bai tava haɗa ta da shi a tsayin lokaci da ta san shi, sannan ta yi alqawarin biya masa bashi da ke kansa matuƙar bai fi qarfinta ba. 

Zuwa wallafa wannan rahoto, jarumar ta cika alƙawari, inda ta biya bashi da daraktan ya bari na fiye da mutane 20.

Ita ma Jaruma Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a ta ɗauki nauyin karatun babban ɗan marigayin a wuyanta, inda za ta cigaba da ɗaukar ɗawainiyarsa dindindin.

Haka nan shi ma fitaccen furodusan Kannywood kuma mamallakin kamfanin Kufaina Film Production da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Bala Mu’azu Kufaina, ya aiko wa iyalan mamacin saqon ya yafe bashin da ke tsakaninsa da marigayin na kuɗin hayar kayan aiki, waɗanda bai samu biya ba kafin rasuwar tasa.

Jarumai irin su Tijjani Asase, Sadiq Sani Sadiq, Tijjani Faraga da kuma takwarorinsa daraktoci irinsu Aminu Saira da furodusoshi kamar Bashir Maishadda da sauransu, sun magantu kan yadda mutuwar ta zo masu da kuma yadda suka ji mutuwar a zuciyarsu.

Daga ƙarshe dukkansu sun yi wa mamacin addu’ar samun dacewa a rayuwar da zai yi ta barzahu zuwa dauwamammiyar rayuwa.

Darakta Bono, wanda ya shahara wajen bayar da umarni a Kannywood, musamman na waƙoƙi masu nishaɗantarwa, ya rasu ya bar mace ɗaya da kuma ’ya’ya uku. Ya yi firamare da sakandire a Kano, sannan ya fara fim a shekarar 1999.

Da fatan Allah Ya gafarta masa, ya yafe kurakuren da ya yi, ya kyautata namu lokacin idan ya zo.

By Editor