Gwamna Lawal ya sha alwashin ganin bayan ‘yan fashin daji a Zamfara

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya sha alwashin kawo ƙarshen ‘yan fashin dajin da suka addabi jihar.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba sa’ilin da ya ziyarci sansanin bai wa Dakarun Rundunar Kare Alumma (CPG) inda suke karɓar horo, shirin da gwamnatin jihar ta ƙirƙiro domin daƙile ‘yan fashin daji a faɗin jihar ta Zamfara.

Cikin sanarwar da ya sanya wa hannu wadda MANHAJA ta samu kwafi, Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce horon da dakarun ke ci gaba da karɓa ya ƙara wa jihar da ma al’ummarta ƙwarin gwiwa dangane da sha’anin yaƙin da ta’addanci a jihar Zamfara.

Sulaiman ya ce tsarin da aka bi wajen tattaro dakarun ba mai sauƙi ba ne, inda aka zaɓo mutum 300 daga kowace ƙaramar hukuma a tsakanin ƙananan hukumomi 14 da jihar ke da su.

Gwamna Lawal ya bayyana ƙwarin gwiwarsa game da samun nasara a fagen yaƙi da matsalar tsaron da gwamnatimsa ke ci gaba da yi, kana ya yi kira ga al’ummar jihar a haɗa kai don ci gaba da wanzar da zaman lafiya a Zamfara.

Yayin ziyarar tasa, Lawal ya ce, “Yau na zo nan ne domin shaida yadda ake ci gaba da bai wa sabbin dakarun kare alumma horo.

“Ina kira a gare ku da ku ba da himma game da horon saboda irin babban aikin da ke gabanku wanda ke buƙatar sadaukarwa don amfani ƙasarmu ta gado.

“Dole mu haɗa kai don cimma kyakkyawan sakamako. Wata rana za mu yi nasarar magance ƙalubalan tsaron da muke fuskanta a faɗin jihar Zamfara.

“Na yi matuƙar farin ciki da abin da na gani a sansanin bada horon. Ya ƙara mini kwarin gwiwa, kuma ina da yaƙinin muna kan turbar da ta dace domin kyautata goben Zamfara,” in Gwamnan.

By Editor