Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Haƙiƙa ko dai yawan tarin takardun kuɗin da su ka kai Naira Tirilyan 27 ba su cika babbar motar ɗaukar kaya wato tireba ba to za su dai cika waje mai faɗin gaske a motar. Ko ni mai rubutun nan ban tava ganin Naira tirilyan a kan takarda ba. Naira tirilyan na nufin Naira biliyan 1000. Naira biliyan na nufin Naira miliyan 1000. Naira miliyan na nufin Naira dubu ɗari sau 10.
Kawai na kiyasta ne yadda yawan kuɗin su ke in an zuba su a ɗaki ko a cikin mota. A watannin baya kafin saukar gwamnatin shugaba Buhari mun ga hotunan da ke nuna lodin kuɗi a mota da su ka rube. Wannan ya faru ne lokacin da gwamnatin ta kawo sabon shirin sauya kuɗi. Ba mamaki indai hakan ya inganta ya zama wasu sun adana kuɗi masu yawan da ba su lura ba har tsawon ajiya ya sa kuɗin sun lalace. Kazalika zai kuma iya yiwuwa kuɗin na babban banki ne da a kan kona don sun ragargaje don haka sai an buga sabbi.
Koma dai yaya lamarin ya ke, faɗuwar darajar Naira ya sa yanzu kusan sai mutum ya kwashi tarin kuɗi a aljifan sa kafin ya iya cefanen gidan sa ko ya iya zuba mai a motar sa. In ma mutum zai kashe kuɗin ta hanyar katin ATM ko turawa ta na’ura to sai ya ƙara sifili ko lambobin sun ƙaru a kan yadda ya saba a baya. Bayan nan da na ke magana bai fi watanni kaɗan ko ma rabin shekara ba. Lamarin ya kara ta’azzara da janye tallafin man fetur da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aiyana a jawabin sa na farko ranar 29 ga watan Mayu.
Ba a daɗe ba sai kawai farashin kayan masarufi ya yi tashin gauron zabi. Yanzu ma abun da ke faruwa shi ne ’yan kasuwar mai ne da kan su kan ƙara farashin tun da gwamnati ta janye hannun ta. Kun ga tun da ba tallafi daga gwamnati ba ma buƙatar yajin aiki ko zanga-zangar neman sassauci. Har yau dai ba a samu sahihin bayanin gwamnatin a watan Agusta ta sanya tallafi don hana farashin litar fetur kai wa Naira 700. A wasu jihohi sayan litar fetur Niara 700 ta tabbata. Gidajen mai masu saukin kuɗi da ke nesa da Legas na sayar da litar Kan Niara 680.
In mutum ya buge da shiga gidajen man gwamnati zai iya samun ragin wasu ‘yan Nairori amma sai ya yi jiran da darajar sa ta kai ladar Nairorin ragin. Wani rubutun da na yi kwanaki na yi hasashen in a ‘yan shekaru mutum na kashe Naira 500 ya samu biyan buƙata to zamanin nan sai Naira 50,000. Sai ma an zo ga abu na wajibi wato kayan abinci mutum zai gane yadda darajar Naira ta sulmuyo. Nawa yau mutum zai zare a aljihun sa ya sayi buhun shinkafa? Da ido na na ga masu sayan buhun shinkafa sun koma auno kwano daya biyu in ya yi yawa goma.
Idan an auno shinkafar sai a riqa haɗawa da ‘yan dabaru don a yi kwana biyu zuwa 5 ba a sake wani awun ba. In shayi ne sai a tsula ruwa da yawa madarar kaɗan don yara su samu dan abun sha kafin tafiya makaranta da safe. Iyayen yara ba ta tasu a ke yi ba. Naira nawa talaka ke buƙata don yin rayuwa kullum a Nijeriya. Ban san ko ma’aunin talauci ya canja daga samun kasa da dala ɗaya a wuni ba. Dole ma ya canja don dalar a lokacin da a ke maganar ba ta fi Naira 450-500-600 ba a bisa misali.
Yau duk da dalar ta haura Naira 1000 a kasuwar canji amma farashin kayan kuma ya haura tashin dalar da ninki biyu ko fiye. Abun damuwa shi ne a na cikin lokacin kakar damunar bana ne inda an yi girbi kayan amfani sun dawo gida. Ko yau ku gwada bincike za ku samu gidajen da sun daina dora tukunya a murhu sai jiran tsammani da ’yan dabarun bakin da Allah ya tsaga.
Ya zama mai muhimmanci duk mai ɗan abun hannun sa ya riqa leƙawa gidajen makwabta ya gano halin da su ke ciki in bai ga tukunya a murhi ba to ya ba da tallafin da ya sauwaƙa. Kowa ya na da garin su ko ƙauyen su, a riƙa shiga wajaje a na kai tallafi duk ƙarancin sa zai taimaka wajen rage matuƙar ƙuncin da wasu da ba sa karɓar albashi ko cinikin kowace haja ke ciki.
Masu karɓar fansho da ke da jibgin nauyi a kan su ma na nan su na fama da yanayin ƙuncin tattalin arziki da ya ƙara ta’azzara don tsanantar tashin kayan masarufi da hakan ya fi ta’allaka da janye tallafin man fetur. Ita kan ta gwamnati na nuna ba za ta iya biyan kuɗin tallafin ba da hakan ya sauya daga dalilan wai wasu ’yan ƙalilan ne ke amfana da tallafin. In ma dai ‘yan ƙalilan ɗin ne talakawa sun gane su na cikin ƙalilan ɗin duk da su ne mafi yawa a cikin ’yan Nijeriya sama da mutum miliyan 200.
Gwamnatin Nijeriya ta shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kasafin kuɗi baɗi 2024 Naira tiriliyan 27.50 wanda hakan ya zama kari ne a kan hasashen farko na kasafin da Naira tiriliyan 1.5.
Ministan kasafin kuɗi Atiku Bagudu ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa da shugaba Tinubu ya jagoranta.
Kasafin ya amince da sanya canjin dala a Naira 700 hakanan ita kuma gangar man fetur kan dala 73.06.
Yanzu dai har gwamnatin na shirin miƙa kasafin ga majalisar dokokin tarayya don amincewa.
Kasafin kuɗin Nijeriya ya dawo aiki daga watan Janairu zuwa Disamba a zamanin gwamnatin Buhari.
Masu sharhi na duba alwashin kamfanin man fetur na NNPCL na fara aikin matatun man Nijeriya daga matatar Fatakwal a watan nan na Disamba.
An haƙiƙance cewa matukar matatun man Nujeriya za su yi aiki to farashin man fetur zai iya saukowa ko da dai ba zai koma yadda ya ke gabanbin janye tallafi ba.
Shugaban kamfanin fetur ɗin Mele Kyari Kolo ya nuna hasashen hakan kuma ga shi lokacin na karatowa.
Nijeriya na da fitattun matatun man fetur a Warri jihar Delta, Fatakwal jihar Ribas da kuma Kaduna a tsakiyar arewacin Nijeriya.
Kolo ya ce a Disamba matatar Fatakwal za ta fara aiki, inda a farkon kwara na baɗi matatar Warri za ta fara na ta aikin yayin da zuwa ƙarshen 2024 ta Kaduna kuma za ta fara aiki.
Matatun man Nijeriya na da ƙarfin tace kimanin ganga miliyan 4.45 a duk wuni.
Mele Kyari a ganawar sa da kakakin majalisar dokoki Tajudeen Abbas ya ce zuwa badin dai da aikin irin su matatar man Dangote Nijeriya za ta dakatar da shigo da mai daga ƙetare kuma ya nuna za ta zama mai fitar da mai kenan baya ga shayar da gida.
A nan kakaki Abbas ya bukaci mika ragamar matatun hannun ‘yan kasuwa don wasu lamuran sai da sa hannun sassa masu zaman kan su.
Farashin gangar man fetur a kasuwar duniya ya dan ragu gabanin taron da ƙungiyar kasashe masu arzikin fetur wato OPEC za ta gudanar.
Gangar ɗanyen fetur mai daraja ta BRENT CRUDE ta sauko da santi 39 inda ta tsaya kan dala 89.19.
Saudiyya da Rasha sun amince bisa raɗin kai na rage adadin man da suke haƙowa don daga darajar gangar man.
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar dokokin Nijeriya wasiƙa don samun hurumin ciwo bashin zunzurutun kuɗi dala biliyan 8.69 da kuma Fam miliyan 100.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas sun gabatar da wasiqar ga ‘yan majalisa.
Wannan neman lamunin dai ƙari ne kan neman hurumin karɓo lamuni da Tinubu ya yi a baya da majalisar ba ta kai ga amincewa da shi ba.
Wsaiƙar da Tinubu ya aika a baya ta ƙunshi neman lamunin dala biliyan 7.86 da kuma Fam miliyan 100.
Takardar ta nuna wannan na daga cikin tsarin cin bashi na shekara ta 2024 mai shigowa.
An tabbatar gwamnatin tsohon shugaba Buhari ita tafi kowace gwamnati a tarihi cin bashi da hakan ya nuna yanzu za a jira a ga zuwa ƙarshen mulkin Tinubu ko zai iya tsallake mizanin ko kuwa a’a.
Kammalawa;
Gaskiyar magana ita ce talakawa na son ganin kasafin kuɗin nan a ƙasa ta hanyar kyautata rayuwar su da samar da sauƙi a duk ɓangarori na abinci, lafiya, tituna, tsaro da duk wani abu da zai sa jama’a su ji a jikin su akwai amfanin gwamnatin dimokraɗiyya a qasar su. In har ‘yan majalisar dokoki, gwamnoni da shugaban ƙasa za su riƙa yawo da manyan sababbin motoci na miliyoyin Naira yayin da talaka ba zai iya tafiya ko da ƙafa ba tare da tsoron wasu tsageru za su tare shi da wuka su kwace ma sa waya ko wata dukiyar sa ba, akwai matsala.
Lalle duk shugaba ya san cewa shi mai hidima ne ga jama’a ta hanyar riqe amanar su. Don haka ba daidai ba ne ya ci abinci ya ture yayin da yara ƙanana a gidajen talakawa ke kwana da yunwa, cutuka da barazanar ’yan ta’adda.
