Hanyoyin da za su taimaka wurin daɗewa a mu’amalar aure

Spread the love

Tare da AMINA YUSUF ALI

Gabatarwa:

Bismillahir Rahmanir Rahim. Maza da yawa suna fama da matsalar kawowa da wuri, ko sun yi magana ko ba su yi magana ba, ya kasance ɗaya daga cikin jirinjiritsin da maza ke fuskanta lokacin mua’amalar aure. Kawowa da wuri shi ne lokacin da namiji ya yi inzali da wuri fiye da yadda ake tsammani ko kuma wasu lokuta (mafi yawa mintuna 2) bayan fara mu’amalar aure. Wasu lokutan inzali da wuri yana faruwa ne saboda rashin ƙwarewa, rashin shiri, rashin lafiya, ko kura-kurai da za a iya kauce wa yayin saduwa.

Wannan babbar damuwa ce ga maza da mata, saboda yana haifar da rashin gamsuwa a tsakanin masurata. Kuma mata sukan fi shan wahala da cutuwa a cikin wannan yanayi. Shi ya sa yake da muhimmanci da kuma wajibi ga maza su shawo kan lamarin. Don matsalar tana rusa zamantakewa ba da wasa ba.

Binciken mu ya nuna cewa, a matsaqaita, yawancin mata sun fi son mazansu su ɗauki aƙalla tsakanin mintuna 10 zuwa 15 yayin farawar, da kuma mintuna 30 idan muka ƙara duka lokacin shiga ciki da kuma lokacin wasanni kafin a tara. Yayin da wasu mata suka ce sun fi son mazajensu su ɗau aƙalla tsakanin mintuna 20 zuwa 40. Kada ka yi mamaki, saboda wasu ba su yarda ba, sun fi son awa 1 ko fiye.

Duk da haka, ba duka mata ba ne, wasu suna da sha’awar jima’i fiye da wasu, wasu kuma sun fi wasu buqata. Wata mintuna 5 sun gamsar da ita, wasu kuma sai an ɗauki awa faya don gamsar da su. Abun dubi a nan shi ne, kuna buƙatar karantar matarka/mijinki muddin kuna son kiyayewa da rinjaye a cikin wannan harkar. Yana da kyau a lura cewa, yana daga cikin ladubban da ɗa’a na Musulunci, gamsar da abokin tarayya. [Ali bin Abi Talib]

Bayan shawarwari da bincike, na sami damar fitar da wasu shawarwari don taimaka muku shawo kan wannan jirinjiritsi. Da fatan za a yi la’akari da shawarwari masu zuwa:

Kafin Saduwa-:

*Ambaton sunan Allah: Abu na farko da ya kamata ku fara shi ne, kiran sunan Allah. Wannan shi ne mafi qarancin. Za ka iya karanta addu’ar da Annabi (SAW) ya kyar lokacin tarawa; “Bismillah, Allahumma jannibnash-shaytan wa jannib-ash-shaytana ma razaƙtana”. Addu’ar za ta kori kowane ɓangare na Shaiɗan daga mu’amalarku. Wasu cututtukan da suka shafi jima’i galibi ana danganta su da kasancewar shaiɗan da aljanu.

*Ƙa’ida ta farko: Kafin ka wadata kanka a gaban matarka, yana da kyau ka sauƙaƙa wa kanka, ma’ana, ka yi fitsari. Lokacin da mafitsara ta cika, tana tilasta maka fitar da maniyyi kafin ka shirya.

*Tsafta: Ita al’aura ba koyaushe take cikin tsabta ba, don haka a tsaftace ta da ruwa ko kuma yin cikakken wanka kafin kusantar juna. Wannan zai haifar da kwanciyar hankali, lafiya da tsaftataccen yanayi gare ku ku biyu.

*Istimna’i ko wasa da al’aura: Wasu masana sun yi bayanin cewa ɗaya daga cikin maganin inzali da wuri shi ne, yin wasa da al’aura kafin saduwa. Wannan na iya faɗuwa ƙarƙashin lokacin wasanni kafin saduwa.

Kafin shigar, mata za ta iya amfani da hannuwanta, harshenta da bakinta don taimaka muku fitar da maniyyi mai zuwa. A cikin haka, Inzali na gaba zai ɗau lokaci mai tsawo kafin ya ƙara haɗuwa.

*Shan magungunan gargajiya: A al’adun Hausawa muna da wata cuta da ake kira “Sanyi”. Abinda ake kira STDs a Turance. Duk da cewa ciwo ne dake rage wa maza da mata yawan sha’awar jima’i, wani lokacin ma yana haifar da bushewar al’aura ko rashin karfin mazakuta. Don haka, akwai magungunan gargajiya da aka fi sani da warkar da irin waɗannan cututtuka. Ko ba ku da lafiya ko kuna da lafiya, ku yi ƙoƙari ku sha waɗannan magunguna, lokaci-lokaci.

Lokacin tarawa

◉ Yin mu’amalar a hankali da farko – Yin komai cikin harshe yana sa jini yana ƙaruwa, kuma nan da nan, za a aika da sigina zuwa ƙwaƙwalwa, sannan dopamine (sinadari a jikin mutum da ke sanya ambaliyar jin daɗi) ba zai yi jinkirin yin aiki ba.

*Lura da iya taku – idan kai mai saurin inzali ne, kiyayewa da iya taku mai kyau zai taimaka maka wajen sarrafa abin, misali, ka san kanka da kyau, ka san yadda da sauri ko kuma a hankali ke saka inzali, don haka ka kiyaye hakan.

*Sarrafa numfashi – Haka na nufin numfashin da kake yi shi ma yana tantance saurin fitar maniyyi. Kada ka ba wa kanka wuya, numfashi a sannu-sannu kuma a hankali. Wani lokaci yin numfashi ba tare da kakkautawa ba na iya yaudarar ka wajen yin inzali da wuri.

Za mu cigaba a wani makon.

Muhammad Ubale Ƙiru masani ne a kan rayuwar ɗan’adam da zamantakewa. Baɗon marubuci ne a wannan shafi na zamantakewa.

By Editor