Daga BASHIR ISAH
An rantsar da tsohon Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, a matsayin sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya.
Lalong ya yi murabus ne daga muƙamin Ministan Ƙwadago a gwamnatin Tinubu sannan ya maye gurbin Napoleon Bali na Jam’iyyar PDP wanda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sauke shi biyo bayan ƙarar da Lalong ya shigar a kansa a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe.
Akawun majalisar, Chinedu Akubueze, shi ne ya rantsar da Long yayin zaman majalisar a ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da Lanlon a matsayin sanata, Akpabio ya yi maraba da Lalong zuwa majalisar, inda ya fada masa cewa, Majalisar wuri ne da duk wanda ya tsinci kansa a cikinta, akan yi amfani da kudinsa da kwarewarsa da dai sauransu, wajen ciyar da kasa gaba.
Zuwan Lalong majalisar karkashin inuwar APC, ya tabbata yanzu majalisa ta 10 na da sanatoci daga APC su 60, yayin da PDP ke da 37, Jam’iyyar Labour 7, NNPP 2, SDP 2, sannan APGA 1, wanda jimillarsu ta kama 109 .
