‘Yan Arewa mu ci gaba da barci!

Hari ko kuma kuskuren da sojoji suka yi na jefa bam a Kaduna ga masu yin Maulidi zai tayar wa da duk wani mai tausayi ko imani hankali.

Ɗauke Batun ɗarikar Addini. Ɗauki ɗan’adamtaka (Humanity). Shin wannan mugun zubar da Jinin bayin Allah da basu ji ba, ba su gani ba. Basa fauke da makami. Bai isa mutum ya zubar da hawayen tausayi gare su ba?.

Idan kana ganin ai ‘yan bidi’a ne akai musu haka kana Jin daɗi a ranka. Kai ma wani lokacin ɗarikar da kake kai za a iya cimmata ta wannan ƙudurin tunda ba mu haɗa kanmu ba. Bare mu san ciwon kanmu.

Mu daina yaudarar kanmu ga ɗariƙu na Addini ko banbancin siyasa ko jinsi idan irin wannan iftila’in ya afkawa Junanmu. Farkon abinda za mu fara kalla shi ne Kalmar Shahada da ta haɗa mu bakiɗayanmu. Sai kuma ɗan’adamtaka (Humanity). Sai kuma mu kalli yankinmu ko da kuwa Kirista aka kashe na Arewa.

Kwanakin baya wani yaron mawaki aka kashe a Asibiti Mohbad (Yaron Naira Merley). Duk gabaɗaya ƙabilun Kudu suka ta da hankalin hatta Majalisar Tarayyar Nijeria. Dole sai da aka saurare su aka bi kadin yadda akai ransa ya salwanta a asibiti. Shin ganganci ne ko shiryawa aka yi duk sai da aka sanya mahukunta suka bincika al’amarin har sai da aka gano gaskiyar maganar yadda akai ya mutu.

Wallahil Azim a lokacin sai da nace ba yaron mawaki ba. A Arewa ko babban Mawaki Kai Ko Malamin addini ne in aka Salwantar da rayuwarsa ta irin wannan salon ransa ya bi Iska. Iyakar abinda za mu iya kawai shi ne Surutu a soshiyal midiya. Shi ma iyakacinmu Facebook da WhatsApp sai Instagram da TikTok. Banda haka ba abinda za mu iya. Da an yi kwana uku za mu ɗauki wani maudu’in.

Shin haka za mu ci gaba da rayuwarmu har zuwa lokacin da barcin da muke zai kai mu ga halaka? Ko muna tunanin a cikin barcin da muke za mu samu waraka ko nasara?

‘Yan Arewa malalata ne kamar yadda tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya Buhari ya kira mu. Babu wani inkahari ga wannan kalmar da ya jingina mana. Yanzu haka a Arewa in ka tari wani da wannan labarin bai ma san anyi kisan kan ba. Wani Kuma ya sani tunda ba a garin da yake abin ya faru ba. Ko kuma tunda ba ‘yan uwansa abin ya shafa ba. shi ba ruwansa. Wani kuma na kallon abin ta fuskar Addini tunda yana kallon Addinin a bai-bai. Tunaninsa tunda ba ‘yan ɗariƙarsa ba ne to shi fa babu abinda ya shafe shi da kisan da akai bare har ya ɓata lokacinsa wajen bibiyar kadin jininsu.

Gaskiyar Magana Ya Kamata ‘yan Arewa mu farka daga wannan nannauyan barcin da muke. Na yi amanna da a Kudu wannan abin ya faru da tuni yanzu Majalisar Tarayya ta magantu kan wannan ɗanyen Aikin da akai musu. Don sai sun tsayar da komai a yankinsu. Hatta Shugaban Ƙasar sai ya ajiye komai da yake ya saurare su.

Rai na mutum 400 har da wani abu ba ƙaramin abu ba ne. Kuma rai na wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Ba sa ɗauke da kowanne irin makami. Wannan abin Allah wadai ne ga ‘yan Arewa da muka kasa haɗa kanmu wajen ganin an daina zubar mana da jinin bayin Allah ‘yanuwanmu.

Abdullahi Jibril Ɗankantoma (UNCLE LARABI) Marubuci ne mai sharhi a kan alamuran yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Kano.