Yadda za ku gamsar da iyalinku yayin mu’amala ta aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI

Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinku na zamantakewa mai zuwa kowanne mako a jaridarku ta Manhaja Blueprint. A makon da ya gabata mun kawo muku wasu bayanai a kan yadda ma’aurata za zu samu damar daɗewa a yayin da suke tarayyar aure. Ba shakka waɗannan dabaru da ƙanina ya rubuto za su taimaka matuƙa wajen samun gamsuwa tsakanin ma’aurata. A makon da ya gabata mun fara kwararomuku bayanai, sai muka tsaya saboda sarari ya cika. Yanzu sai ku gyara tabaronku don cigaba da karanta bayanai daga makon da ya gabata. A sha karatu lafiya.

  • Hutawa/Sassautawa – idan kun huta, tsokar jikinku ma tana shakatawa tana kasancewa ba a takure ba, haka ma kwakwalwarku. Sassautawa da yi kamar kuna yin wani nau’i na aiki. Hakan yana kiyaye kwararar jini kuma ana sarrafa shi. Ba za a aika saƙonnin warya zuwa ƙwaƙwalwa don sakin sinadarin ‘dopamine’ ba.
  • Tazara – Da zarar ka fara jin buƙatar kawowa, ka ɗan dakata ka huta. Kada ks zauna kawai, amma fa ba zama kawai haka ba. A mai da hankali ga wasanni ko wasu abubuwa tsahon mintuna 2 zuwa 4 za ku iya dawowa ku ci gaba.
  • Canja Salon mu’amalar – Babu shakka, wasu salon kwanciyar sun fi wasu kyau idan ana maganar jin daɗin jima’i. Kada ku fara da salon da kuka san zai iya sa ku saurin inzali. Sai dai idan kun ji kun kai wata ƙuloluwar matsayi na jin daɗi, sai ku yi sauri ku canza zuwa wani salon.

*Tunaninka kamanninka – Masana ilimin halayyar dan adam sun yi imanin cewa jima’i ba koyaushe yake a kan vangarorin al’aura ba. Ƙololuwar jin daɗi ana sarrafa shi ne ya fito daga ƙwaƙwalwa. A lokacin jima’i, mata da miji suna barin tunanin haka ya rinjaye su. Idan ka cire tunaninka daga gare shi, ka guje wa tarkon da za ka faɗa na sauri sakin sinadarin ‘dopamine’ da wuri. Yayin da ake saduwa, yi ƙoƙari ka karkatar da tunanin zuwa abubuwa, kamar aikinka, kasuwanci, fim, ko wani abu da ke tsoratar da ku; wani abu da zai sa a kore ku daga wurin aikin. A cikin haka, kuna tsawaita sha’awar sakin maniyyi da wuri.

◉ Dabarar kwaroron roba mai kauri – Rororon roba mai kauri yana taimakawa sosai wajen tauye jin daɗin mai yawa. Don haka, yana hana jini dake aika sako zuwa ƙwaƙwalwa. Hakan na iya saku samun tsawaita inzali.

◉ Matse kan alaura – duk lokacin da ka ji ka kusa kawowa, cire alaurarka, sannan ka matse ƙasan kan. Watau, matse ƙasan kan azzakarin na tsawon daƙiƙa 10. Wannan dabarar tana hana kawowa a lokacin.

◉ Kallon Sha’awa ga abokin zama – abu ne na al’ada ga mace da namiji su yi tunanin juna yayin tarayywa. Yawan wannan tunanin na iya motsa dopamine wanda zai sa ku sakinsa da wuri.

◉ Tasirin nishi na mata da numfashi – Shi ma so samu a rage ko a daina don yana da tasiri wajen saurin kawowa.
Bayan Tarawa
*Motsa jiki – babban maganin matsalar rashin qarfin mazakuta da da saurin kawowa, shi ne motsa jiki. Ƙarfafan maza lafiyayyu suna daɗewa a mu’amalar aure fiye da sauran nau’ikan maza. Motsa jiki yana taimaka maka ka ƙona sukari da kitsen da ke zaune a cikin mafitsara kuma yana sa ka so ka saki ‘Dopamine’ da sauri.

*Wanke al’aura bayan saduwa -duk lokacin da kuka sadu da iyalanku kuka gama, sai ku tsaftace al’aurarku sannan ku ɗaura alwala kafin tafiya zagaye na biyu ko na uku. Yana daga cikin sunnar Annabinmu masoyinmu (S.A.W). Yin jima’i a kai-a kai ba tare da tsaftacewa yana haifar da tavarɓarewar da rashin ƙarfin mazakuta.

◉ Yin amfani da man ‘Lubricant’ – Suna da kyau don suna sauƙaƙa mu’amalar aure sannan suna hana yawan amfani da ƙarfi domin yawancinsu suna da sinadarai masu rage yawan kuzari dake hana ka jin matsananciyar sha’awa. Don haka, tasirinsu yana rage saurin inzali. Man Durex Classic ya fi dacewa, saboda ba shi da mai mai yauƙi da sinadarin hana haihuwa. Ba shi da wata illa.

◉ Shan ruwa da yawa – Ruwa yana aiki wajen cire ma’anidai masu illa daga jiki. Lokacin da kuke shan isasshen lita na ruwa a rana, yana fitar da duk abubuwan da ba a so a cikin jinin ku, don haka yana haɓaka kuzarinku.

◉ Sanin abincin ku – Wasu nau’ikan abinci da abubuwan sha da muke ci suna da illa ga rayuwar jima’i. Misali sugar, lemunka kwalba masu gas, tarkacen abinci wanda ba su da nau’ikan gina jiki, da dai sauransu. Suna rage sha’awar jima’i kuma suna haifar da rashin kuzari ga namiji.

*Yin mu’amala akai-akai (Be Regular) – Ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da fitar maniyyi da wuri shine idan aka dau lokaci mai tsawo ba tare da saduwa ba. Yin jima’i a kai-a kai yana taimaka maka qarin karfin tsokan wajen da kuma ba ka ƙarfin juriya. Abunda nake nufi da mu’amala a kai-a kai shi ne, aqalla sau 5 zuwa 7 a mako. Amma duk da haka, Ali binu Abi Talib ya ce yawan jima’i yana kashe mutum ko kuma ya sa shi saurin tsufa.

Bayani a kan mata Lokacin saduwa

*Har tsawon wani lokaci mace ke son namiji ya kasance? Amsar wannan tambayar shi ne, matsakaicin adadin mata sun fi son lokacin jima’i ya kasance aƙalla, watau mintuna 10 zuwa 15. Wasu sun fi son ya fi haka. Don haka, ku karanci mazajenku yadda kuke koyon dabarun aikinku.

*Yaya tsawon lokacin da suke ɗauka kafin su yi inzali? Babu tabbataccen amsa ga wannan tambayar. Ya bambanta daga mace zuwa mace. Amma dabarunku a cikin wasanni kafin saduwa na iya ƙayyade yadda suke saurin inzali ko akasin haka.

  • Jima’i wasa ne ga mata – mace ba za ta ji daɗin kusanci ba idan tana baƙin ciki ko cikin damuwa. Wannan shine dalilin da ya sa yana da kyau a sa su farin ciki koyaushe kuma a taimaka musu wajen rage damuwa. Damuwa tana sa su daina sha’awar jima’i kuma a wasu lokuta yana shafar al’aurar su ta bushe. Idan tana so, tana jin daɗi, idan ba ta so, za ta ji zafi ne da rashin jin daɗi yayin saduwa.

*Shin mata suna yin inzali? Eh wasu matan suna inzali kamar maza, duk ya dogara da abin da kuke musu don tada musu sha’awa da sauri kuma da abunda kuke musu su kai ga kololuwar sha’awa da jin dadi. Idan ka iya da kyau kuma ka san abin da za ka yi don faranta mata rai, tabbas za ta yi inzali.

◉ Me ke sa mata sha’awa? Wannan tambaya ɗaya ce da ta farko, babu amsa takamaimai. Mata kala-kala ne, kuma mata daban-daban suna da wuraren jin daɗi daban-daban. Da fatan Allah ya zaunar da dukkan ma’aurata lafiya a gidajensu. Ku cigaba da karatun Blueprint Manhaja.

Muhammad Ubale Ƙiru baƙon marubuci ne a wannan filin na Zamantakewa a wannan makon. Muna godiya.