A sake duba yanayin huɗubarmu a ƙasar Hausa

Daga MUHAMMAD AMINU IDRIS

Huɗubar Jumu’a ko cin muntunci? Huɗubar Jumu’a ko hassada? Huɗubar Jumu’a ko bidi’a?

Na ga wani Malami kuma Dakta, ban sani ba ko na ilimi ne ko na likitanci ne, ya yi sama da awa ɗaya a kan munbarin Jumu’a yana cin mutuncin ɗan uwanshi malami kuma Farfesa, kuma wai da sunan huɗubar jJumu’a yake yi! Lallai wannan abin kunya ne, abin baƙinciki ne kuma abin a yi Allah wadarai da shi ne tunda da sunan Musulnci yake yi.

Annabi (SAW) ya yi gaskiya da ya ce: “babu ilimi idan babu aiki da shi.” Kuma ya ce: “Allah ba ya ƙwace ilimi kamar yadde yake ƙwace (sauran abubuwa), sai dai yana ƙwace shi ne da karɓar rayukan malamai.

Har sai ya zamo babu sauran malami, sai wasu (jahilai masu da’awar ilimi) su ba da fatawa ba tare da ilimi ba. Sai su ɓace kuma su ɓatar.”

Lallai mun fara tunkarar wannan zamanin domin a yanzu an mai da munbarin huɗuba wajen kamfen din siyasa, wajen zagi da cin mutuncin mutane, musanman malamai da ‘yan siyasa. Saboda rashin kunya da rashin tsoron Allah har kiran sunan mutane su waɗannan shaiɗanun malaman suke yi, su kuma jahilan mabiyansu suna ta kabbara.

Allah ya yi gaskiya da ya ce: “Masu jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne malamai.”

Lallai idan waɗannan mutanen masu da’awar “malunta” da kuma ” Ahlussunna” ba su ji tsoron Allah sun daina zagi, da wulaƙanta mutane, da kuma cin mutuncinsu da sunan huɗuba ko wa’azi domin biyan wata buƙata tasu ba, toh Allah zai shafe darajarsu, da kimarsu, da mutuncinsu Ya kuma wulaqanta su tun a duniya kafin a je lahira Ya jefa su cikin wutar jahannama! Allah Ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.

Muhammad Aminu IDRIS, Member Royal Institute of Biomedical Sciences, London. Ya rubuto daga Ƙasar Italiya.